Jerin kasashe 20 aka akafi arhan man fetur a duniya, Najeriya ce ta 7
Ministar kudi, kasafin kudi da shirye-shiryen kasa, Zainab Ahmad Shamsuna, ta bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zata cire tallafin man fetur a 2022.
Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur zai yi tashin gwauron zabo.
A madadin wannan tashi, Ministar kudin ta bayyana cewa Gwamnati za ta fara rabawa talakawan Najeriya dubu biyar-biyar a wata matsayin kudin mota.
Legit.ng Hausa ta ta tattaro wasu Jerin kasashe 20 aka akafi arhan man fetur a duniya kawo Nuwamban 2021 bisa lissafin Shafin Global Petrol Prices.
Ga jerinsu (Lita):
1. Venezuela - $0.000
2. Iran - N24.66 ($0.060)
3. Syria - N94.941 ($0.231)
4. Angola - N112.78 ($0.274)
5. Algeria - N136.25 ($0.331)
6. Kuwait - N142.83 ($0.347)
7. Nigeria - N165.89 ($0.403)
8. Turkmenistan - N176.18 ($0.428)
9. Kazakhstan - N188.11 ($0.457)
10. Malaysia - N210.70 ($0.490)
11. Iraq - N211.58 ($0.514)
12 Bahrain - N218.16 ($0.530)
13. Haiti - N220.22 ($0.535)
14. Bolivia - N223.52 ($0.543)
15. Ethiopia - N225.16 ($0.547)
16. Qatar - N237.5 ($0.577)
17. Colombia - N239.98 ($0.583)
18. Azerbaijan - N242.044 ($0.588)
19. Egypt - N242.044 ($0.588)
20. Saudi Arabia - N255.62 ($0.621)
Asali: Legit.ng