Da Ɗumi-Ɗumi: Ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda ba zai canja komai ba, Sheikh Gumi
- Malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya ce ayyana yan bindiga a matsayin yan bindiga ba zai canja halin tsaro da ke ciki a kasar ba
- Babban malamin ya ce dama tun kafin ayyanawar jami'an tsaro na yakar yan bindigan kamar yadda suke yakar yan ta'adda ne
- Gumi ya bada misali da ayyana IPOB a matsayin yan ta'adda yana mai cewa hakan bai canja komai ba a kasar
Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya ce ayyana yan bindiga matsayin 'yan ta'adda kawai mataki ne da aka dauka na siyasa, Vanguard ta ruwaito
Ya ce gwamnatin tarayya ta yarda wani sashi na kafafen watsa labarai a kasar suna juya ta, yana mai cewa hakan ba zai kawo wani sauyi a kasa ba.
Ya ce:
"Ina tunanin gwamnatin tarayya ta bari kafafen watsa labarai na wani yanki a kasar nan suna juya ta.
Na yi farin ciki da aka kama ni, na san laifi na ke yi, in ji mai kaiwa 'yan bindiga bayanan sirri a Zamfara
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ba zai kawo wani canji ba a kasa domin tun kafin a ayyana su dama ana yakar su ne kamar 'yan ta'adda."
A hukuncin da ta yanke Mai Shari'a Taiwo Taiwo ta ce barnar da kungiyoyin 'Yan Bindiga da 'Yan Ta'adda ke yi ta'addanci ne.
Gumi, cikin sanarwar da hadiminsa Malam Tukur Mamu, Dan-Iyan Fika ya fitar ya ce:
"Wannan kawai suna ne kuma na yi imanin ba zai canja komai ba a kasa.
"Idan ka tuna, IPOB ita ma an ayyana ta a matsayin kungiyar ta'addanci. Har takardan kotu ta tabbatar da haka, amma kasashen duniya ba su yarda da ayyana IPOB a matsayin kungiyar ta'addanci da FG ta yi ba."
"Bai samar da sakamakon da ake bukata ba. Ba a hana su zuwa kasashen waje ba, suna nan a matsayin yan kasa. Wane irin ayyana wa ne wannan?."
Ya cigaba da cewa:
"Ina fatan 'yan Nigeria ba za su dauki makiyaya a matsayin 'yan ta'adda ba amma su dauka cewa akwai bata gari cikinsu idan aka kwatanta da nagari kamar yadda muka ke ganin harin IPOB kan hukumomin tsaro da wasu yan arewa a matsayin ta'addanci. Kalilan cikin makiyaya ne 'yan fashin daji idan ka duba adadinsu"
Sheikh Gumi: Za a yi nadamar ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda
Tun a baya, Shiekh Ahmad Gumi ya ce masu ikirarin yin jihadi daga kasashen waje na iya shigowa Nigeria idan aka ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda.
Tun da baya, malamin ya taba rokon gwamnatin tarayya ta yi wa 'yan bindigan afuwa sannan ta basu tallafi don sauya halayensu su kama sana'a.
Da ya ke tsokaci kan kiraye-kirayen da ake yi a baya-bayan nan na neman a ayyana 'yan bindiga a matsayin yan ta'adda, Gumi, cikin sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, akwai abubuwa masu hatsari da ka iya biyo baya.
Asali: Legit.ng