'Kada ku mayar da Jigawa kamar Spain', Gwamna Badaru ya yi barazanar dawo da kullen korona

'Kada ku mayar da Jigawa kamar Spain', Gwamna Badaru ya yi barazanar dawo da kullen korona

  • Gwamna Muhammadu Badaru na jihar Jigawa ya nuna damuwarsa kan yadda mutanen jiharsa ke gudun yin riga kafin korona
  • Badaru ya ce idan har mutanen ba su sauya ba zai sake dawo da dokar takaita zirga-zirga don kada cutar da sake dawowa kamar wasu kasashen waje
  • Gwamnan ya kuma yi kira da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautun gargajiya a jiharsa su dage wurin wayar da kan al'umma

Jigawa - Gwamna Muhammad Badaru na jihar Jigawa ya yi barazanar sake dawo da dokar takaita zirga-zirga domin dakile yaduwar cutar COVID-19 a jiharsa sakamakon jan kafa da mutane ke yi wurin karbar rigakafin.

Gwamnan, wanda bisa alamu ya damu, ya yi wannan jawabin ne yayin da taron kaddamar da yin rigakafin COVID-19 da aka yi a karamar hukumar Kiyawa a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Rayuka 9 sun salwanta a sabon farmakin da miyagun suka kai Plateau

'Kada ku mayar da Jigawa kamar Spain', Gwamna Badaru ya yi barazanar dawo da kullen korona
Gwamna Muhammadu Badaru na jihar Jigawa. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Bayanai sun nuna cewa mutane 122,200 ne suka karbi riga-kafin karo na farko a jihar amma guda 53,753 ne kacal kawo yanzu suka koma suka karbi allurar rigakafin ta biyu, rahoton Daily Trust.

Gwamnan, wanda ya ce ba za a amince da hakan ba, ya sha alwashin ba zai bari a mayar da Jigawa tamkar Spain da wasu kasashen waje ba inda cutar da sake bazuwa saboda sakacin mutane.

Badaru ya shawarci ciyamomi da masu sarauta su wayar da kan mutane

Badaru, ya bawa al'ummar jihar tabbacin cewa rigakafin bata da wani illa, yana mai cewa ba zai aikata wani abu da zai jefa rayuwar al'ummarsa cikin hatsari ba.

Ya ce:

"Idan kun tuna Shugaba Muhammadu Buhari, mataimakinsa da iyalansu duk sun yi riga kafin.

Kara karanta wannan

Shaidar EFCC: Da kaina na ciro wa Jang biloyoyin naira babu takarda

"A matakin jiha, dukkan ku kun ga lokacin da na yi nawa rigakafin tare da mataimaki na da sauran iyalan mu da manyan jami'an gwamnati kuma har yanzu babu abin da ya same mu."

Daga karshe, Badaru ya bukaci shugabannin kananan hukumomi, masu sarautun gargajiya su tabbatar sun cigaba da wayar da kan mutane game da riga kafin musamman tasirin sa ga zamantakewa da tattalin arzikin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: