Borno: 'Yan gudun hijira sun bar sansanoninsu kafin cikar wa'adin da gwamnati ta bada
- ‘Yan gudun hijira da ke Maiduguri sun tashi daga sansanoninsu tun kafin ranar 30 ga watan Nuwamba da gwamnatin jihar ta yanke za ta rufe
- Bayan manema labarai sun kai ziyara wasu daga cikin sansanoninsu, an samu rahoto akan yadda yawancinsu suka watse
- An samu rahotanni akan yadda gwamnatin jihar a ranar Asabar ta raba musu kudade da kayan abinci don su ci gaba da rayuwa a gidajensu cikin walwala
Borno - Tuni ‘yan gudun hijira mazauna Maiduguri suka fara kwashe komatsansu suna komawa gidajensu bayan gwamnatin jihar ta sanar da ranar 30 ga watan Nuwamba ya zama ranar kulle sansanoni.
Wakilin NAN ya kai ziyara sansanoninsu a ranar Laraba, rahotanni sun nuna cewa da yawansu sun nufi gidajensu.
NAN ta tattaro bayanai akan yadda a ranar Asabar gwamnatin jihar ta samar da kudade da kayan abinci ga ‘yan gudun hijiran duk don shirye-shiryen rufe sansanonin don su ci gaba da rayuwa a gidajensu.
Sai dai wasu ‘yan gudun hijira daga Gwoza, Monguno da karamar hukumar Guzamala sun sanar da NAN a Maiduguri cewa, an ba magidanta N100,000 sannan aka ba matan aure N50,000 don ci gaba da rayuwa a gidajensu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mustafa Gubio, kwamishinan gyare-gyare da gine-ginen jihar ya ce rufe sansanonin cikin Maiduguri ya na cikin ayyukan wani bangare na ma’aikatarsa.
Gubio ya ce ‘yan gudun hijira daga sansanin Bakassi sun kai 7000 ake kyautata zaton zasu koma kananun hukumominsu don su ci gaba da rayuwarsu.
“Shirin komawa gidajensu ma a cikin tsarin Kampala Convention zasu yi,” a cewar Kwamishinan.
Zulum a sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi, ya bai wa masu komawa gida N.5b
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya gwangwaje ‘yan gudun hijira fiye da mutane 5000 da rabin biliyan daya, Daily Trust ta ruwaito.
‘Yan gudun hijiran sun nuna bukatar komawa gidajensu ne don su cigaba da rayuwa. Gwamnan ya isa sansanin ‘yan gudun hijiran da misalin 5:45am inda aka fi sani da Bakassi a Maiduguri.
A takardar wacce hadimin gwamna Zulum ya saki, ya ce gwamnan ya yi sa’o’i 7 ya na jagorantar raba kudade da kayan abinci yayin da ya kai ziyarar ta ba-zata don tallafa wa mabukata da marasa gida saboda wasu mutanen su na zuwa sansanin ‘yan gudun hijiran tun safe sai dare su ke komawa gidajensu da sunan su ‘yan gudun hijira ne.
Asali: Legit.ng