Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu kan wata hazikar yarinya da ta ci A a WAEC, ta samu 345 a Post UTME
- Wata yar Najeriya daga jihar Imo, Chiemela Stephanie Madu, ta samu sakamako mai daraja ta farko a dukkan darussan da ta zauna a WAEC
- Yarinyar ta samu nasarar cin maki 345 cikin 400 a jarabawar share fagen shiga jami'a Post UTME a jami'ar FUTO
- Mafi yawan yan Najeriya da suka tofa albarkacin bakin su, sun yaba wa hazakarta, wasu kuma suka bada labarin nasu sakamakon
Imo- Wata yarinya mai hazaka yar Najeirya, Chiemela Stephanie Madu, ta sha yabo daga yar uwarta bisa kyakkyawan sakamakon da ta samu a jarabawan da ta zauna guda biyu.
Mhiz Olamma ta rubuta a shafinta na dandalin sada zumunta Facebook, cewa Stephanie ta jefa iyalan gidansu cikin tsantsar farin ciki da alfahari bayan ta samu A a baki ɗaya darussan WAEC.
Ina son zama kwararriyar likita
Dalibar wacce ta fito daga jihar Imo, ta kuma samu maki 345 a jarabawar Post UTME da ta zauna ta jami'ar fasaha ta tarayya dake Owerri (FUTO).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Stephanie ta bayyana cewa kullum mafarkinta da fatanta shine ta karanci aikin kwararren likita (Medicine) a ƙasar Canada.
Yan Najeriya da dama sun garzaya wurin rubutun, sun tofa albarkacin bakinsu game da bajintar da yarinyar ta nuna a jarabawan.
Yayin da instablog9ja suka buga labarin a shafin Instagram, Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu daga cikin martanin yan Najeriya.
Kasali_wells yace:
"Ta yi kokarin sosai fa, ɗalibar makarantar gwamnati ta samu wannan sakamako, ina taya ki murna."
Officialbsolomon yace:
"Sakamakon da ta samu a jarabawar JAMB kwata-kwata bai yi kama da wanda ta samu a WASSCE ba."
domingo_loso yace:
"Ta nuna bajinta matuka, nawa sakamakon WAEC da NECO sun yi kyau, na samu B da C a darussan dana zauna."
real_stainlezz yace:
"Zan yi takaici idan naji labarin cewa yarinyar nan ta kare a buɗe shagon POS... wannan kasar tawa."
hrmking_zino yace:
"Wata yar ɗan uwana ma haka ta samu A a dukkan darussa, ina ganin jarabawan WAEC ta yi kyau wannan shekarar."
A wani labarin kuma JAMB ta bankado yadda akai ciwa-ciwan bada Admishin 706,189 a manyan makarantun Najeriya
Hukumar JAMB ta bankado yadda manyan makarantun gaba da sakandire suka bada gurbin karatu 706,189 ba tare da bin doka ba.
Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, yace laifin ya karade makarantu daga kowane yankin Najeriya 6 da ake da su.
Asali: Legit.ng