Hukumar kwastam ta yi ram da tulin Tramadol a filin jirgin saman dakon kaya
- Hukumar kwastam a jihar Legas ta kame wasu kaya na kwayoyin Tramadol a wani filin jirgin saman dakon kaya
- Hukumar ta ce ta kame kwayoyin Tramadol kimanin miliyan 1.5 da suka kai darajar Naira miliyan 92.3
- Hukumar ta kuma bayyana irin ci gaba da take samu a jihar Legas ta hanyoyi daban-daban da suka shafi aiki
Legas - Jami’an hukumar kwastam ta Najeriya a ranar Talata sun kama kwayoyin Tramadol kimanin miliyan 1.5 a filin jirgin saman dakon kaya na jihar Legas, Channels Tv ta ruwaito.
Jami’an hukumar kwastam ta yankin Murtala Mohammed ne suka kama kayayyakin a rumfar shigo da kaya ta SAHCO dake Legas.
Da yake jawabi ga manema labarai, kwamandan yankin Murtala Mohammed, Sambo Dangaladima ya ce duk da cewa ba a kama wanda ake zargi ba, an kama kayayyakin da kudinsu ya kai Naira miliyan 92.3 domin ci gaba da bincike.
Hukumar a baya ta kama kunshin tabar wiwi 404 da darajarsu ta kai miliyan 32 a jihar Sokoto, Daily Trust ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hukumar kwastam a Legas na kara samun ci gaba a Legas
Kwanturola Dangaladima ya bayyana cewa a cikin watanni biyar da ya karbi mukamin kwamandan yankin, adadin kudaden shiga ya karu zuwa Naira biliyan 3 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Ya alakanta karuwar kudaden shiga da samun hadin kai da goyon baya daga masu ruwa da tsaki da kuma kwazon jami’an hukumar.
Kwamandan ya kuma yi kira ga dukkan jami’an rundunar da masu ruwa da tsaki da su hada kai domin yaki da masu fasa kwauri domin amfanin kasa baki daya.
A cewarsa:
“Ba mu da wata kasa sai kasar nan. Duk inda ka je, kai dan kasa ne na biyu, don haka dole ne mu zauna mu yi abin da ya dace ko da menene."
Hukumar kwastam ta mika gurbattun magunguna na miliyoyi da ta kwata ga NAFDAC
A wani labarin, Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta, ta karbi kayayyakin magunguna marasa rajista da darajarsu ta kai Naira miliyan 100 da Hukumar Kwastan ta kama.
Kwanturola a sashin B na sashin ayyukan kwastam na tarayya, Al-Bashir Hamisu ne ya mika kayayyakin ga NAFDAC a Kaduna, Daily Nigerian ta ruwaito.
Mista Hamisu ya ce rukunin masu sintiri na kan iyakokin kwastam sun kwace kayayyakin magungunan ne a watan Agusta.
Asali: Legit.ng