Cire tallafin fetur, haraji, cin bashi, da shawarwari 6 da bankin Duniya ya ba Gwamnatin Tarayya
- Babban bankin Duniya ya ba Najeriya wasu shawarwari da nufin farfado da tattalin arzikin kasar
- Daga cikin wadannan shawarwari akwai maganar janye biyan tallafin man fetur da aka dade ana yi
- Bankin na Duniya yana so a kara haraji a kan wasu kaya na musamman domin a samu kudi a 2022
The Cable ta tattaro wadannan shawarwari kamar haka:
1. Lafta haraji a kan wasu kaya
Babban bankin na Duniya ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara harajin da ke kan sugari, giya da lemu. Wannan mataki zai bunkasa asusun kudin shigan Najeriya.
2. A janye tallafin man fetur
IMF da bankin Duniya sun hadu a kan wannan shawara ta kashe tallafin man fetur. Masanan su na ganin tallafin ya fi amfanar masu kudi, kuma ana asarar tiriliyoyin kudi.
3. A rage cin bashi
Masanan bankin Duniya sun ce bashin da ke wuyan Najeriya zai fara yi mata yawa nan da 2025 idan aka tafi a haka, don haka aka bukaci a rage cin bashi daga CBN.
4. Kasuwar canji
Idan gwamnatin Muhammadu Buhari ta bi shawarar bankin, za ta gyara farashin kudin kasashen waje. A halin yanzu farashin kudin kasar waje su na nan barkatai.
5. Bude iyakoki
Wata shawara da aka bada ita ce a bude iyakokin kasan Najeriya domin a iya shigo da kaya daga ketare. Ana sa ran yin hakan zai rage tsadar kaya da ake fama da shi.
6. Komawa fasahar zamani
Ana so nan a shekarar 2022, Najeriya ta rungumi fasahohin zamani. Wannan zai kawo cigaba ta fannin kasuwanci, karfafa harkokin mata da inganta tsaro a kasa.
7. Ceci mai karamin karfi
Idan aka janye tallafin fetur, za ayi fama da tsadan kaya, don haka aka bada shawarar a kawo manufofin taimakon marasa galihu, musamman raba masu kudi.
8. Gyara aikin tashoshi
An yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo karshen jinkirin da ake samu wajen shigo da kaya ta tashoshin Najeriya. Wannan kabali da ba’adi su na dakusa kasuwanci.
Tattalin arziki: Naira ta yi kasa
A makon nan ne aka ji farashin Naira ya zazzago zuwa N555. Hakan ya na nufin an rasa kimanin N20 cikin kwana uku, daga ranar Juma’ar da ta wuce zuwa Litinin.
Yayin da kirismeti yake karasowa, an ji Dalar Amurka ta doke Naira a kasuwar BDC ta ‘yan canji. Ana sa ran Dalar za ta karye ne domin za a rika aiko kudi daga ketare.
Asali: Legit.ng