Budurwa ta fasa kwalba ta caka wa direban motar haya saboda kudin mota a Legas

Budurwa ta fasa kwalba ta caka wa direban motar haya saboda kudin mota a Legas

  • An samu rahoto akan yadda wani direban mota, Adewale ya zargi fasinjarsa, Laura da sharba masa fasassar kwalba bayan wata hayaniya ta shiga tsakaninsu a wuraren Agungi da ke Ajah cikin Legas
  • Adewale ya shaida yadda ya dauko ta daga Ajao Estate zuwa gidan kawarta a Ajah a ranar Talata da nufin za ta biya shi kudin mota N4,100 idan sun isa
  • Sai dai ta ce ta yi kokarin tura masa kudaden ta asusun bankinta amma abin yaci tura sai ta shiga wurin kawarta ta dauko N2,000 wacce ya ki amincewa da ita daga nan rikici ya barke tsakaninsu

Jihar Legas - Wani direban mota mai suna Adewale ya zargi fasinjar sa, Laura da daba masa fasassar kwalba yayin wata hayaniya a wuraren Agungi da ke Ajah a jihar, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Budurwa ta gurfanar da tsohon saurayinta a gaban kotun musulunci a jihar Kaduna

An samu bayanai akan yadda Adewale ya dauki budurwar daga Ajao Estate zuwa gidan kawarta da ke Ajah a ranar Talata.

Budurwa ta fasa kwalba ta caka wa direban motar haya saboda kudin mota a Legas
Budurwa ta caka wa direban motar haya kwalba a Legas. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Punch ta rahoto yadda bayan isarsu wurin, direban ya bukaci kudinsa amma budurwar tace ta kasa tura wa ta wayarta.

Yayin tattaunawa da manema labarai, direban mai shekaru 42 ya ce fasinjar ta shiga cikin gidan kawarta ta dawo da N2,000.

Rashin amincewarsa da N2,000 ne ya janyo fadan

Ya ce ya bukaci ta biya shi kudin shi N4,100 daga nan suka hau hayaniya wanda ya sa Laura ta datse shi da fasassar kwalba bayan ya hana ta tafiya.

Kamar yadda Adewale ya ce:

“Da misalin karfe 12pm na ranar Talata, wata budurwa, Laura ta bukaci in kai ta Agungi da ke Ajah daga Ajao Estate. Kuma na dauketa na kai ta har Ajah din.

Kara karanta wannan

Kada ka janye dokar hana shigo da shinkafar kasar waje, Gwamnan APC ga Buhari

“Bayan isarmu wurin, na ajiyeta kuma kamar yadda kudin ya nuna ta wayar ya kamata ta biya ni N4,100 a matsayin kudin mota. Amma sai tace ta kasa turawa ta wayarta don haka ta bukaci mu shiga wurin kawarta ni kuma na ki nace ta shiga mota ta in kaita inda zata ciro kudi ta biyani.
“Ta ki yarda da hakan sai ta shiga cikin gidan ta dawo da N2,000 a maimakon N4,100 sannan ta bukaci in bata lambar asusun banki na don ta tura min sauran amma na ki amincewa.”

A cewarsa har fashewa ta yi da dariya

Ya kara da bayyana yadda ya bukaci ta biya shi kudi ba tare da bata lokaci ba sai ta fara dariya. Tana shiga gidan ta dawo da kwalba a hannunta.

Ya ce tana kokarin kara shigewa ta bar shi sai ya riketa kawai ta kai masa farmaki da kwalba. Inda yace ta fasa kwalbar ta yanke shi a hannu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An tsinta gawar limamin Abuja kusa da gona

Ya bayyana yadda wani dan jihar Ogun ya kai shi kemis don a duba masa lafiya sannan ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda.

Wani jami’in tsaro da ke yankin wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana yadda yana tsaka da bacci ya ji direba da fasinjar su na fada sannan ya mike ya yi kokarin sasanci tsakaninsu.

Jami’in tsaron ya ce tabbas ta yi amfani da kwalba

Ya shaida cewa ya ga su na fada amma bai san yadda aka yi budurwar ta ji wa mutumin ciwo ba. Amma ya ce tabbas yarinyar ta yi amfani da kwalba.

Ya shaida cewa ta je ganin kawarta Blessing ne, sannan sai da ya kira kawar ya nuna mata aika-aikar da kawarta ta yi.

Jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan, CSP Adekunle Ajisebutu ya ce an sanar da ‘yan sanda komai akan lamarin.

A cewarsa yanzu haka Laura tana hannun hukuma kuma ana ci gaba da bincike akan yadda lamarin ya auku.

Kara karanta wannan

Jagoran APC a Neja ya shawarci Buhari da ya tsige Lai Mohammed daga kujerar minista

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: