Shirin karin farashin mai: N200bn zamu rika kashewa a wata wajen rabawa yan Najeriya N5000

Shirin karin farashin mai: N200bn zamu rika kashewa a wata wajen rabawa yan Najeriya N5000

  • Gwamnatin tarayya ta lashi takobin kawo karshen lamarin biyan kudin tallafin mai daga shekarar 2022
  • Jami'an gwamnatin Shugaba Buhari sun sanar da cewa farashin mai zai tashi a 2022 amma yan Najeriya su kwantar da hankulansu
  • Gwamnati tace za ta kashe raran kudin da za'a samu sakamakon haka wajen rabawa talakawan Najeriya

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce za ta rika kashe N200 billion a wata wajen rabawa talakawan Najeriya kudi domin rage zafin da cire tallafin mai zai haifar.

Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur zai yi tashin gwauron zabo.

Leadership newspaper ta ruwaito cewa Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan ne ranar Talata, 23 ga Nuwamba 2023 a taron kaddamar da rahoton Bankin Duniya (NDU).

Kara karanta wannan

Farashin mai na iya tashi N340 ga Lita a sabon shekara idan aka cire tallafi, GMD na NNPC

A cewarta, talakawan dake Najeriya mutum guda milyan 30 zuwa 40 za'a rika baiwa wannan kudi wata-wata.

Tace amma sai an cire tallafin za'a san adadin yan Najeriya da zasu samu wannan kudi.

N200bn zamu rika kashewa a wata wajen rabawa yan Najeriya N5000
Shirin karin farashin mai: N200bn zamu rika kashewa a wata wajen rabawa yan Najeriya N5000
Asali: UGC

Farashin mai na iya tashi N340 ga Lita a sabon shekara, GMD na NNPC

Dirakta Manaja na kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari, ya tofa nasa albarkacin bakin kan lamarin cire tallafin man fetur a sabuwar shekarar 2022 da ake fuskanta.

A nasa jawabin, ya bayyana sabon farashin man da ake sa rai na iya konawa tsakanin N320 da N340 ga lita, rahoton Vanguard.

A cewarsa, da tun shekarar 2020 za'a cire tallafin amma wasu matsaloli suka taso kuma aka fasa hakan.

Yace amma daga 2022, doka ta wajabtawa gwamnati cire tallafin gaba daya.

Kara karanta wannan

Dukkan gwamnoni mun yarda Gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur, Nasir El-Rufa'i

Gwamnonin sun yi ittifaki kan wannan lamari

El-Rufa'i yace dukkan gwamnonin Najeriya sun yarda gwamnatin tarayya ta janye daga biyan tallafin mai.

A cewarsa:

"Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta gana kuma an amince a marawa gwamnatin tarayya baya ta janye tallafin mai a Febrairu, kuma tayi amfani da kudin N250 billion a wata a rabawa yan NAjeriya kudin."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng