Dukkan gwamnoni mun yarda Gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur, Nasir El-Rufa'i
- Gwamna Nasir El-Rufa'i yace dukkan gwamnonin Najeriya sun yarda Gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur
- A cewarsa nan da watan Febrairu suka fadawa Gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur gaba daya
- El-Rufa'i yace kasashen dake makabtaka da Najeriya da masu kudi kadai ke amfana da tallafin mai
Abuja - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya bayyana cewa gaba daya Gwamnonin Najeriya sun amince Gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur a sabon shekara.
El-Rufa'i ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar a taron World Bank Nigeria Development Update (NDU) ranar Talata, rahoton TheCable.
El-Rufa'i yace Najeriya na asarar N250 billion a wata kan kudin tallafi kuma duk da haka yan Najeriya basu amfana.
A cewarsa, kasashen dake makwabtaka da Najeriya irinsu Kamaru sun fi amfana da tallafin man fiye da yan Najeriya.
Yan Najeriya sun fi bukatar Kalanzir
A cewar Gwamnan na Kaduna, yan Najeriya sun fi bukatar Kalanzir fiye da man fetur.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace:
"Man da yan Najeriya suka fi bukata shine Kalanzir, kuma an cire tallafinsa kuma babu abinda ya faru. Man da masana'antu da manyan motoci ke amfani Diesel ne kuma an cire tallafi, babu abinda ya faru."
"A watan nan, N14bn kadai NNPC ta kawo asusun gwamnati. A kasafin kudi, N120bn ya kamata su kawo a wata, amma 14bn suka kawo da barazanar cewa zasu bukaci Gwamnati ta basu kudin tallafi."
"Wa ke amfana da tallafin fiye da yan sumoga, kasashen afrikan dake makwabtaka da mu, da kuma masu kudi?"
Gwamnonin sun yi ittifaki kan wannan lamari
El-Rufa'i yace dukkan gwamnonin Najeriya sun yarda gwamnatin tarayya ta janye daga biyan tallafin mai.
A cewarsa:
"Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta gana kuma an amince a marawa gwamnatin tarayya baya ta janye tallafin mai a Febrairu, kuma tayi amfani da kudin N250 billion a wata a rabawa yan NAjeriya kudin."
Zamu kara kudin mai, amma zamu fara baiwa yan Najeriya N5,000 kudin mota a wata: FG
Ministar kudi, kasafin kudi da shirye-shiryen kasa, Zainab Ahmad Shamsuna, ta bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zata cire tallafin man fetur a 2022.
Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur zai yi tashin gwauron zabo.
A madadin wannan tashi, Ministar kudin ta bayyana cewa Gwamnati za ta fara rabawa talakawan Najeriya dubu biyar-biyar a wata matsayin kudin mota.
Asali: Legit.ng