ISWAP na ƙokarin kafa daular ta a Jihar Neja, Gwamnatin jiha

ISWAP na ƙokarin kafa daular ta a Jihar Neja, Gwamnatin jiha

  • Gwamnatin jihar Neja ta koka akan yadda ISWAP ta ke yunkurin kafa daularta a karamar hukumar Borgu da ke cikin jihar
  • Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Minna
  • Hakan ya biyo bayan korafin da shugaban karamar hukumar Shiroro, Hon Suleiman Chukumba ya yi inda ya ce ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga sun mamaye wurin garuruwa 500

Jihar Neja - Gwamnatin jihar ta koka akan yadda ISWAP take yunkurin kafa daularta a karamar hukumar Borgo da ke jihar, The Nation ta ruwaito.

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a Minna inda yace kungiyar ce ke da alhakin garkuwa da mutane a Dodo da ke Wawa.

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno

ISWAP na kokarin kafa daular ta a Jihar Neja, Gwamnatin jihar
Gwamnatin Jihar Neja ta ce ISWAP na kokarin kafa daula a jihar. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Nation ta bayyana yadda ya sanar da cewa kungiyar ISWAP tana shirin kafa daularta a wuraren babbar tashar Kainji da ke karamar hukumar Borgu.

Wannan ya biyo bayan yadda Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya sanar da yadda ‘yan Boko Haram suka mamaye wasu bangarorin jihar.

‘Yan Boko Haram sun kwace kusan anguwanni 500 a jihar

Har ila yau shugaban karamar hukumar Shiroro, Honorable Suleiman Chukwumba ya koka akan yddada ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga yanzu haka suka kwace kusan anguwanni dari biyar.

A cewar Matane, gwamnatin ta san harkokin da kungiyar take yi ne ta mazauna yankin inda ‘yan kungiyar suke fada musu cewa ba ‘yan bindiga bane su, Ubangiji ne ya turo su.

Kamar yadda Matane ya ce:

“Su kan ce ba ‘yan bindiga bane su, amma so suke yi su kafa daularsu a babbar tashar Kainji. Su na cewa Ubangiji ne ya turo su kuma daga iyakar jamhuriyar Nijar, Benin da Najeriya suke yin ayyukansu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnati ta haramta siyar da babura a wata jihar arewa

“Duk da jamhuriyar Benin ta rufe iyakarta, ISWAP na harkokinta ta cikin anguwannin da ke kusa don su tabbatar jama’a sun amince da koyarwarsu sannan sun manta da batun gwamnati.”

Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri

A wani rahoton, Mai garin Lokoja, Alhaji Mohammed Kabiru Maikarfi III, ya dakatar da yin duk wani sha’ani da dare a cikin garin Lokoja da duk wasu anguwanni da su ke da makwabtaka da Lokoja har sai yadda hali ya yi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya bayar da umarnin nan ne sakamakon yadda ya ga bata gari su na amfani da damar shagulgulan dare wurin cutar da jama’a a cikin babban birnin jihar.

Kungiyoyin asiri su kan yi amfani da damar bukukuwan dare da sauran sha’anoni a Lokoja da kewaye wurin kai wa jama’a farmaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: