EFCC ta sake gurfanar da dan uwan Saraki da tsohon kwamishinan Kwara
- A ranar Litinin, hukumar yaki da rashawa reshen jihar Kwara ta kara gurfanar da Ope Saraki, dan’uwan tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki gaban kotu
- Ba shi kadai ta gurfanar ba har da kwamishinan labaran jihar Kwara, Olatunji Oyeyemi Moronfoye, bisa zarginsu da wawurar dukiyar al’umma
- Dama an fara shari’ar ne tun watan Mayun 2015 a gaban alkali Olayinka Faji na babbar kotun tarayya ta jihar inda aka dinga canje-canjen alkalai
Kwara - Hukumar yaki da rashawa ta EFCC reshen jihar Ilori, a ranar Litinin ta gurfanar da Ope Saraki, dan’uwan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kuma tsohon kwamishinan labarai na jihar Kwara, Olatunji Oyeyemi Moronfoye a gaban kotu.
Daily Trust ta ruwaito cewa, hakan ya biyo bayan zarginsu da amfani da ofishinsu ta hanyar da bai dace ba, yasar kudin al’umma da halasta kudin haram.
Zasu tsaya gaban alkali Muhammed Sani na babbar kotun tarayya dake zama a Ilori, Daily Trust ta ruwaito.
Dama an fara shari’ar ne tun ranar 13 ga watan Mayun 2015 a gaban Alkali Olayinka Faji na babbar kotun tarayya da ke Ilorin ne, inda aka dinga samun koma baya saboda canje-canjen alkalai.
EFCC ta zargi Ope, tsohon hadimi na musamman na MDGs a jihar, akan amsar N11,180,000.00 daga wani Kunle Adimula.
Kudin ya wuce da yawan da za a biya wani mutum.
Kuma laifin ya ci karo da sashi na 1(a) da 16(1)(d) na satar kudade(haramcinsa) doka ta 2011 (wacce aka gyara) kuma hukuncin na karkashin sashi na 16(2)(b) na dokar.
Kamar yadda EFCC ta bayyana, Moronfoye yayin da yana mai bada shawara na musamman na MDGs, an zarge shi da bayar da kwangilar gina asibitin Ijagbo da kuma kai magunguna ga asibitoci 2 da ke jihar Kwara ba bisa ka’ida ba.
Ana zargin laifin ya ci karo da shashi na 58(4) kuma hukucin na karkashin sashi na 58(5)(a) da (b) na dokar Public Procurement 2007.
Duk wadanda ake zargin basu amsa laifukan da aka karanto musu ba.
Bayan rokonsa, lauyan EFCC, Sesan Ola, ya bukaci kotu ta duba lamarin kuma ta kullesu a gidan gyaran hali.
Sai dai Sulyman Abaya da Joshua Olatoke, SAN, masu kare Ope Saraki da Moronfoye, sun bukaci kotu ta bayar da belinsu.
Alkali Sani bayan sauraron lauyoyin, ya amince da bayar da belinsu bisa wasu sharudda.
Alkali Sani ya dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Fabrairun 2022, don sauraron karar Ope Saraki da kuma ranar 22 Fabrairun 2022 na Moronfoye.
Alkali Faji a ranar 13 ga watan Muyun 2015 ya amince da belin Moronfoye da Saraki da N50,000,000 da kuma tsayayyu 2.
Asali: Legit.ng