Labari da duminsa: Jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya kama da wuta, mutane da dama sun mutu

Labari da duminsa: Jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya kama da wuta, mutane da dama sun mutu

  • Wani jirgin ruwa da ya dako fasinjoji da kayansu ya kama da wuta a Bonny/ Bille/Nembe Jetty, Fatakwal, jihar Rivers
  • Wasu da abin ya faru a gabansu suna kyautata zaton wani ne ya sha sigari ya jefar a cikin jirgin
  • Ana fargaban fasinjoji da dama sun rasu sakamakon gobarar da ta fara ci tun misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin

Jihar Rivers - Ana fargabar mutane da dama sun mutu a lokacin da jirgin ruwa mai jigilar kaya ya kama da wuta a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers, The Nation ta ruwaito.

Jirgin, da aka fi sani da jirgin kasuwa, yana dauke da 'yan kasuwa ne zuwa wani wurin da ba a sani ba a lokacin da ya kama da wuta a kusa da Bonny/ Bille/Nembe Jetty a Fatakwal.

Kara karanta wannan

Ruwan kudi: Bidiyon yadda wasu mutane suke ta kwasar kudade a kan titi a Amurka

Labari da duminsa: Mutane da dama sun mutu yayin da jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya kama da wuta a Rivers
Mutane da dama sun mutu yayin da jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya kama da wuta a Rivers. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Gobarar da ta fara ci tun misalin karfe 10 na safiyar Litinin, har yanzu bata mutu ba a lokacin hada wannan rahoton.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, har yanzu ba a gano abin da ya yi sanadin gobarar ba amma wasu da abin ya faru a gabansu suna zargin wani mai shan sigari ne ya yi sakaci ya jefar da sigari ba tare da ya kashe ba a jirgin.

Wata ganau ta ce ana kyautata zaton wata mata da yaranta uku da ke cikin jirgin sun mutu.

Jaridar The Nation ta gano cewa daya daga cikin wadanda aka ceto daga jirgin ya samu munanan kuna.

Wannan shine karo na biyar da ake samun gobarar jirgin ruwa a jihar tun karshen mako.

Wasu da abin ya faru a idonsu sun ce jirgin ruwan ya saba daukan kimanin mutanen 50 tare da kayansu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Mai kula da sarrafa jiragen sama ya yanke jiki ya fadi, ya mutu ya na tsaka da aiki

Ba a gano abin da ya yi sanadin gobarar ba a lokacin hada wannan rahoton.

Yadda ginin Ikoyi mai hawa 21 ya rushe, Leburan da ta rutsa da shi ya magantu

A wani rahoton, daya daga cikin wadanda su ka samu nasarar tsira yayin da ginin bene mai hawa 21 na Ikoyi ya rushe ya bayar da bayani akan yadda lamarin ya auku, bisa ruwayar Premium Times.

A cewar sa, ya na tsaka da aikin gyaran wani ginshikin ginin tare da abokin aikin sa a kasa su ka fara jin ginin ya na rushewa.

A hirar da Premium Times ta yi da shi ya ce an bukaci ya yi shiru akan lamarin don gudun abinda zai iya biyo baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: