Hankula sun tashi a jihar Nasarawa kan kisan wasu makiyaya
- Jama'a na cikin halin fargaba da zullumi bayan wasu tsagerun yan bindiga sun kashe wasu makiyaya biyu a garin Ashige, karamar hukumar Lafiya da ke jihar Nasarawa
- An dai tsinci gawarwakin makiyayan ne a cikin wani gona inda fuskokinsu ke dauke da sara
- An tattaro cewa lamarin ya afku ne a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba
Jihar Nasarawa - An fara samun tashin hankali a Ashige, karamar hukumar Lafiya da ke jihar Nasarawa, sakamakon kashe wasu makiyaya biyu da wasu yan bindiga suka yi.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mummunan al’amarin ya afku ne a daren ranar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba.
Rahoton ya kawo cewa an tsinci gawarwakin makiyayan ne a wani gona dauke da shaidar sara a fuskokinsu.
An ajiye gawarwakin nasu a asibitin kwararru na Dalhatu Araf da ke garin Lafiya.
Miyagun ya bindiga sun hallaka mutun 213, sun yi garkuwa da wasu 676 a jihar Katsina
A gefe guda, gwamnatin jihar Katsina, ranar Alhamis tace yan bindiga sun kashe mutum 213, sun sace 676 a faɗin kananan hukumomin da matsalar tsaro ta shafa, jihar Katsina.
This Day ta rahoto gwamnatin na cewa yan bindigan sun aikata wannan ta'adi ne tsakanin watan Yuli zuwa Octoba, 2021.
Gwamnatin ta kara da cewa a wannan tsawon lokacin jami'an tsaro sun samu nasarar damke mutum 724 da ake zargi da aikata ta'addanci kan mutane a jihar.
A wani labarin, yan ta'adda da aka fi sani da yan bindiga sun nada wasu mambobinsu a matsayin dagatai a wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.
A cewar wata jaridar intanet ta Sokoto, Daily Star, kasurgumin shugaban yan bindiga, Turji ne ya nada sabbin dagatan.
Rahoton ya ce an fara kiran yan ta'addan su kira yan kauyen Gangara su hallarci taro a kauyen Suturu a ranar Alhamis inda aka sanar da sauke tsaffin dagatan sannan suka nada mambobinsu a matsayin sabbin shugabanni.
Asali: Legit.ng