Yadda ‘yan mata 7 da ke dawowa daga Maulidi suka rasu a hatsarin jirgin ruwa a Jigawa

Yadda ‘yan mata 7 da ke dawowa daga Maulidi suka rasu a hatsarin jirgin ruwa a Jigawa

  • Hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadin rasuwar 'yan mata bakwai a jihar Jigawa a ranar Alhamis, 18 ga watan Nuwamba
  • Lamarin ya afku ne a lokacin da 'yan matan ke kokarin tsallake wani kogi a hanyarsu ta dawowa daga taron Maulidi da aka yi a garin Gasanya
  • Hakimin kauyen Gafasa, Alhaji Adamu Abdullahi, ya ce tuni aka binne yaran

Jihar Jigawa - Wani abun bakin ciki ya afku a jihar Jigawa a daren ranar Alhamis, 18 ga watan Nuwamba, lokacin da wani jirgin ruwa ya nitse, inda wasu 'yan mata bakwai suka rasa ransu.

A bisa ga rahoton sashin Hausa na BBC, lamarin ya afku ne a lokacin da 'yan matan ke kokarin tsallake wani kogi a hanyarsu ta dawowa daga taron Maulidi da aka yi a garin Gasanya.

Kara karanta wannan

Shugaban Najeriya Buhari zai ba Gwamnoni 36 bashin Naira Biliyan 650 da za a karba a 2051

Yadda ‘yan mata 7 da ke dawowa daga Maulidi suka rasu a hatsarin jirgin ruwa a Jigawa
Yadda ‘yan mata 7 da ke dawowa daga Maulidi suka rasu a hatsarin jirgin ruwa a Jigawa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

An tattaro cewa jirgin na dauke da mutane 12 ne lokacin da ya kife a tsakanin kananan hukumomin Auyo da Kafin Hausa, inda bakwai suka rasu, sauran biyar din kuma suka tsallake rijiya da baya.

Wata majiya ta ce:

"Suna a kan hanyarsu ta komawa gidansu a Gafasa da ke karamar hukumar Kafin Hausa daga Gasanya a karamar hukumar Auyo."

Malam Mikail Jibril, daya daga cikin iyayen wadanda suka rasu, ya ce yaran suna a tsakanin shekaru 11 da 12.

Hakimin kauyen Gafasa, Alhaji Adamu Abdullahi, ya ce tuni aka binne yaran, ruwayar Vanguard.

Ni da mahaifiyata muna kallo lokacin da aka zare ran kanina amma babu yadda muka iya - Dangote

A wani labarin, mun kawo a baya cewa mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya magantu a kan rasuwar kaninsa, Alhaji Sani Dangote.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda aka hallaka mutane 52 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Marigayin wanda ya kasance mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya rasu a ranar Lahadi, 14 ga watan Nuwamba, a kasar Amurka bayan ya yi jinya.

Da ya tarbi jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke Kano, a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba, Dangote ya ce mahaifiyarsu da yaran Sani na a wajen da aka dauki ran marigayin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng