Da ana sayan rai da kudi, da mun kashe ko nawa ne don ceton Sani Dangote - Tinubu

Da ana sayan rai da kudi, da mun kashe ko nawa ne don ceton Sani Dangote - Tinubu

  • Manyan yan siyasa da jami'an na cigaba da tururuwa zuwa jihar Kano don gaisuwar ta'aziyya ga iyalan Dangote
  • Babban Attajiri, Aliko Dangote, ya yi rashin kaninsa kuma abokin aikinsa, Sani Dangote a farkon makon nan
  • Dangote ya bayyana yadda suka ji lokacin da aka fada musu sai da suyi hakuri, kaninsu tafiya zai yi

Kano - Jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yi kiraga iyalan Alhaji Aliko Dangote su rungumi kaddara bisa rasuwar Sani Dangote.

Tinubu yace da ana iya ceton rai da kudi, da sun tara ko nawa ne domin ceton ran Sani Dangote.

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayinda ya ziyarci Alhaji Aminu Alhassan Dantata, babban yaya ga mamacin, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Hotuna: Ganduje ya jagoranci manyan yan siyasa wajen tarbar Tinubu yayin da ya isa Kano don ta’aziyyar Dangote

A cewar Tinubu,

"Mutuwa na nuna ikon Allah. Ba kudi ba. Da kudin na sayan rai, da ko nawa zamu biya."
"Babu abinda wani zai iya. Haka Allah ya kaddara. Haka yaso. Kuma babu mai iya canzawa."
"Mun zo ne domin tayaka jaje ko zaka dan ji sanyi. Ka sani kana da sauran yara. Allah ya baka tsawon rai da isasshen lafiya kuma Allah ya yiwa Sani Dangote Aljannah Firdous."

Da ana sayan rai da kudi, da mun kashe ko nawa ne don ceton Sani Dangote - Tinubu
Da ana sayan rai da kudi, da mun kashe ko nawa ne don ceton Sani Dangote - Tinubu
Asali: UGC

A nasa jawabin, Alhaji Alhassan Dantata ya mika godiyarsa ga tawagar Tinubu.

Daga baya Tinubu ya garzaya gidan Attajiri, Aliko Dangote, babban yayan mamacin a gidansa dake Kano.

Hakazalika kuma ya samu rakiyar gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, inda suka kai ziyara wajen Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, kuma suka halarci Sallar Juma'a a Fada.

Kara karanta wannan

Bukatar sakin Nnamdi Kanu babban lamari ne, amma zan yi shawara: Buhari ga Dattawan Igbo

Ni da mahaifiyata muna kallo lokacin da aka zare ran kanina amma babu yadda muka iya - Dangote

Alhaji Aliko Dangote, ya magantu a kan rasuwar kaninsa, Alhaji Sani Dangote.

Marigayin wanda ya kasance mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya rasu a ranar Lahadi, 14 ga watan Nuwamba, a kasar Amurka bayan ya yi jinya.

Dangote ya ce mahaifiyarsu da yaran Sani na a wajen da aka dauki ran marigayin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng