Bukatar sakin Nnamdi Kanu babban lamari ne, amma zan yi shawara: Buhari ga Dattawan Igbo

Bukatar sakin Nnamdi Kanu babban lamari ne, amma zan yi shawara: Buhari ga Dattawan Igbo

  • Shugabannin kabilar Igbo daga kudu maso gabas sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ofishin shugaban kasa da ke fadar Villa
  • Sun gabatar da bukatar sakin Nnamdi Kanu dake tsare hannun hukumar tsaron DSS yanzu haka
  • Gwamnatin tarayya tace zata caji Kanu da laifin dukkan yan sandan da ake kashewa a yankin Kudu maso gabas

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sakin Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar yan ta'addan IPOB ya sabawa dokar da ta baiwa sashen Shari'a karfin cin gashin kanta.

Buhari ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin manyan dattawan Igbo wanda ya hada da Tsohon Minista Sufurin Sama kuma tsohon dan majalisa, Chief Mbazulike Amaechi.

Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Shugabannin Igbo sun gana da Buhari a fadar Villa

Buhari yace:

"Ka gabatar da bukata mai wuyan gaske a kaina matsayin Shugaban kasar nan...Tun da na zama shugaba shekaru shida da suka gabata babu wanda zai ce na yi shisshigi cikin aikin Shari'a."
"Wannan bukata na da nauyin gaske. zan yi shawara."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari ga Dattawan Igbo
Bukatar sakin Nnamdi Kanu babban lamari ne, amma zan yi shawara: Buhari ga Dattawan Igbo Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Dattijon Igbo, Cif Mbazulike Amaechi wanda ke da shekaru 93 ya roki Shugaba Buhari ya taimaka ya saki Nnamdi Kanu kuma yayi alkawarin Kanu zai daina abubuwan da yake yi.

A cewar Adesina, Cif Amaechi Yace:

"Ba zai sake babatun da yake yi ba. Ba wai don ina da alaka da su (IPOB) ba, amma ana girmama ni a kasar Igbo a yau."

Dattijon ya kara da cewa sau biyu yana haduwa da Nnamdi Kanu kuma ya sauraresa.

Shugabannin Igbo sun gana da Buhari a fadar Villa

Kara karanta wannan

Ko kwana guda ba zan nemi kari ba idan wa'adi na ya kare: Buhari ga Sakataren Amurka

Manyan shugabanni daga yankin kudu maso gabas sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ofishin shugaban kasa da ke fadar Villa, Abuja, a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba.

Dattijo Hon. Mbazulike Amaechi ne ya jagoranci tawagar wacce ke dauke da tsohon gwamnan jihar Anambra, Dr. Chukwuemeka Ezeife.

Har ila yau a tafiyar akwai mataimakin shugaban kungiyar zaman lafiya na addinai, Bishop Sunday Onuoha, Mista Tagbo Amaechi, da Chief Barr. Goddy Uwazurike.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da ministan kwadago da daukar ma'aikata, Chris Ngige, ministan kimiya da fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu, ministan harkokin waje, Mista Geoffrey Onyeama da kuma ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajuiba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng