Bidiyo da hotunan gasar karatun Al-Kur'ani da rundunar 'yan sanda ta shirya a Kano a tsakanin jami'ai
- Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta shirya gasar karatun Al-Kur'ani a tsakanin jami'anta da ke aiki a jihar Kano
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, a halin yanzu ana ci gaba da gasar, wanda za a kammala yau Alhamis
- An gudanar da gasar karatun ne a karkashin jagorancin kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Sama'ila Shu'aibu Dikko
Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta shirya gudanar da gasar karatun Al'Kur'ani tsakanin jami'an 'yan sandan da ke aiki a jihar Kano.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a cikin wani bidiyo da ya yada a shafinsa na Facebook a ranar Laraba 17 ga watan Nuwamba, 2021.

Source: Facebook
A cewar Kiyawa, ana gudanar da gasar karatun ne a hedkwatar 'yan sanda da ke Bompai a jihar Kano, a karkashin jagorancin kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Sama'ila Shu'aibu Dikko.
A cikin bidiyon, Legit.ng Hausa ta gano lokacin da Kiyawa yake yiwa jama'a bayanin abin da ke faruwa, inda aka nuna jami'in dan sanda na karanta Al-Kur'ani a gaban alkalan gasa.
Kalli bidiyon:
A wani sabon bidiyon da Kiyawa a sake da safiyar ranar Alhamis, ya bayyana cewa, ana kokarin kammala gasar Al-Kur'anin, kuma nan kusa kadan za a bayyana sakamakon gasar.
Kana, Legit.ng Hausa ta tattaro hotunan lokacin da ake gudanar da gasar, wanda jami'in hulda da jama'a, Abdullahi Haruna Kiyawa ya yada a Facebook.
Kalli hotunan:
Yadda tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kano ya canza gidan siyasa sau 6 a shekara 7
A wani labarin, Jaridar Daily Trust ta rahoto Farfesa Hafizu Abubakar yana bayanin abin da ya sa ya bar tsagin mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bi tawagar G7.
Hafizu Abubakar yace ya bi tawagar masu adawa da tsagin gwamnati ne domin su ne a kan gaskiya, yace suna tafiya da kowa a siyasance yadda ya kamata.
“Maganar gaskiya abin da ke faruwa a jam’iyyar APC, abin takaici ne. Ba haka mu da duk magoya bayanmu, muka sa rai ba.” - Hafizu Abubakar.
Asali: Legit.ng

