Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro 100 a jihar Benuwai

Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro 100 a jihar Benuwai

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya nuna rashin jin dadinsa bisa kisan da ake wa jami'an tsaro dake kokarin kare mutane
  • Ortom yace sama da jami'an tsaro 100 ne suka rasa rayukansu a jihar cikin shekaru biyu da suka gabata
  • Yace wasu na kokarin shiga tsakaninsa da shugaban kasa, amma ya zama wajibi ya farka daga baccin da yake yi

Benue - Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, yace miyagun yan bindiga sun kashe jami'an tsaro sama da 100 a kan bakin aiki cikin shekaru biyu da suka shude.

Punch ta rahoto cewa gwamnan ya faɗi haka ne yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Ortom yace damuwarsa da abinda ke faruwa ne yasa ya faɗi cewa wasu makiyaya na shigowa daga kasashen waje, waɗan da ke shirin kwace Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ba Buhari shawara ya yi watsi da kudirin da Majalisa za ta kawo gabansa

Gwamna Ortom
Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro 100 a jihar Benuwai Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Jami'an tsaro a jihar Benuwai sama da 100, wanda suka haɗa da DSS, yan sanda, NSCDC da sauransu aka hallaka a kokarin su na tabbatar da zaman lafiya a jihar da ƙasa baki ɗaya, wannan kalubale ne babba."

A cewarsa dukkan yan Najeriya suna da alhakin kare kasar nan daga hannun yan ta'adda domin goben yara da ma waɗan da ba'a haifa ba.

Wane mataki ya kamata a ɗauka?

Gwamna Ortom ya kara da cewa duk wanda kaji yace wai komai na tafiya dai-dai a Najeriya to ba karamin munafiki ba ne.

Ya kuma jaddada cewa idan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yana da kudiri mai kyau, to waɗan da suke kewaye da shi ne suka kwace ragamar shugabancin kasan.

Ortom yace ya zama wajibi shugaban ƙasa ya tashi tsaye ya binciki abinda ke faruwa kuma ya ɗauki matakin gaggawa.

Kara karanta wannan

Abun Mamaki: An kama mahaifi da abokinsa dumu-dumu suna lalata da 'yayansa mata biyu

Kazalika ya bayyana cewa makusantan Buhari na aiki ba dare ba rana domin haɗa shi faɗa da shugaban ƙasa.

"A koda yaushe ina girmama shugaban ƙasa duk lokacin da na samu damar tattaunawa da shi."
"Na faɗa masa gaskiya game da fulani makiyaya, amma kuna ganin tsarin zamanantar da kiwo da ya fara a shekarar 2016."

A wani labarin kuma Mutum 5 sun kone kurmus yayin da tanka makare da mai ta fashe a Ibadan-Legas

Wani mummunan hatsari da ya yi sanadiyyar fashewar Tankar dakon mai ya lakume rayukan akalla mutun 5.

Rahoto ya bayyana cewa Tanka makare da man fetur ta yi taho mu gama da wata babbar mota a hanyar Ibadan-Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262