Ba haka aka haifeni ba, Samari ko sha'awa ta ba sa yi: Budurwa ta bayyana a bidiyo
- Duk da matsalar nakasa da take fama da shi, kyakkyawar budurwa mai shekaru 24 ya bayyana cewa tana alfahari da kanta kuma duk namijin da ya aureta ba karamin dadi zai ji ba
- Chiwetalu yar aji 3 ce a tsangayar lissafin kudi a jami'ar Kimiya da Fasaha ta jihar Enugu (ESUST)
- A hirar da tayi, ta bayyana cewa ba haka aka haifeta ba amma kaddara ya hau kanta kuma ba'a samu waraka ba
Enugu - Wata budurwa yar Najeriya, Chiwetalu Charity, wacce aka yankewa kafa ta bayyana cewa samari basu shawa'ar jerawa da ita saboda halin da ta samu kanta.
Chiwetalu wacce yar aji 3 ce a tsangayar lissafin kudi a jami'ar Kimiya da Fasaha ta jihar Enugu (ESUST) ta bayyana cewa wani mutumi da ya taba fita da ita yace mata shi fa ji yake kamar yana tafiya da yar karamar yarinya.
Ba haka aka haifeni ba
Chiwetalu ta bayyanawa BBC News Pidgin cewa ba haka aka haifeta ba, kawai an wayi gari ne aka lura jini bai gudana cikin kafafunta kuma suka fara rubewa.
Tace an tafi asibitoci daban-daban don neman waraka amma daga baya aka bada shawaran guntule kafafun domin ceton rayuwarta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ina alfahari da kaina
Budurwar ta bayyana cewa duk da halin da take ciki da kuma tsangwamar da take fuskanta wajen maza da mata, tana alfahari da kanta.
A cewarta, duk namijin da ya aureta ba karamin dadi zai ji ba.
Sabuwa fil a leda nake, ban taba sanin ‘da namiji ba har nayi aure – Amarya mai shekaru 55
A wani labarin kuwa, wata 'yar Najeriya da ta kusa cire tsammani, domin sai da ta kai shekaru 55 kafin Allah ya bata mijin aure.
Allah ya kulla aure tsakanin matar mai suna Esther Bamiloye da angonta Isaac Bakare mai shekaru 62 wanda shima wannan ne aurensa na farko.
A wata hira da tayi da jaridar Punch, Esther ta bayyana cewar duk da dadewar da tayi ba tare da aure ba, ta yi kokarin ganin ta kare mutuncinta, domin a cewarta bata taba sanin 'da namiji ba kafin aurenta. Ta ce ita budurwa ce sabuwa fil a leda.
Asali: Legit.ng