Shugaban majalisar dattawa da manyan gwamnati sun isa jihar Kano domin jana’izar Sani Dangode
- Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya isa garin Kano domin halartan jana'izar Sani Dangote
- Ahmad ya isa jihar ne tare da wasu manyan sanatoci a safiyar yau Laraba, 17 ga watan Nuwamba
- Ya bayyana mutuwar marigayin a matsayin babban rashi ga Najeriya da nahiyar Afrika
Jihar Kano - Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da sauran manyan masu ruwa da tsaki ciki harda 'yan majalisa sun isa jihar Kano a safiyar ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba.
Sun yi wa garin Kano tsinke ne domin halartan jana'izar mataimakin shugaban rukunin kamfanin Dangote, Sani Dangote, wanda ya rasu a ranar Lahadi.
Allah ya yi wa Sani wanda ya kasance kani ga mai kudin Afrika, Aliko Dangote, rasuwa a ranar 14 ga watan Nuwamba, a kasar Amurka bayan ya yi fama da 'yar rashin lafiya.
Lawan ya tashi daga babbar birnin tarayya Abuja inda ya samu rakiyar Sanata Sani Musa, Sanata Bello Mandiya, Sanata Tokunbo Abiru da kuma Alhaji Auwal Lawan (Sarkin Sudan Gombe).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai ba shugaban majalisar dattawan shawara a kafofin watsa labarai, Ola Awoniyi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, rahoton Punch.
A cikin sanarwar mai taken 'Shugaban majalisar dattawa a Kano don jana'izar Sani Dangote', Lawan ya bayyana marigayin a matsayin babban dan kasuwa da ya kawo ci gaba ga tattalin arzikin Najeriya da Afrika.
A ruwayar Nigerian Tribune, Lawan ya kuma bayyana mutuwar nasa a matsayin babban rashi ga Najeriya da Afrika duba ga kokarin rukunin Dangote wajen ganin ci gaban kasar da nahiyar.
An bayyana dalilin da yasa gawar Sani Dangote ba ta iso Najeriya daga Amurka ba
A wani labarin, mun kawo a baya cewa gawar marigayi Sani Dangote ba ta iso daga Amurka ba har a yammcin Talata sakamakon wasu cike-ciken takardu da ba a yi ba.
Wata majiya daga iyalan ta sanar da Daily Trust cewa ana tsammanin za a kawo gawar Kano a ranar Laraba.
An samu bayanai akan yadda lokaci ya tafi ba a taho da gawar Sani Dangote ba, kanin attajiri Aliko Dangote, sakamakon wasu takardu da ake ta cikewa.
Asali: Legit.ng