Abun Mamaki: An kama mahaifi da abokinsa dumu-dumu suna lalata da 'yayansu mata biyu

Abun Mamaki: An kama mahaifi da abokinsa dumu-dumu suna lalata da 'yayansu mata biyu

  • Kotu ta kama wani magidanci tare da abokinsa da aikata laifin lalata da yayansa na tsawon lokaci a jihar Gombe
  • Mutanen da aka gurfanar ana tuhuma, sun musanta zargin da ake musu tare da gabatar da shaidu guda biyu
  • Sai dai mai gabatar da kara kuma lauyan gwamnatin Gombe, Hafsat Aliyu Abubakar, ta gabatar da shaidu 6

Gombe - Wata kotu dake zamanta a jihar Gombe ta yanke wa mahaifi tare da abokinsa hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon shekaru.

Aminiya ta rahoto cewa Kotun ta ɗauki matakin ne bayan kama su da laifin keta haddin yayan magidancin biyu na tsawon lokaci.

Mai Shari'a Joseph Ahmed Awak, ya kama mutanen guda biyu da aikata laifin cin zarafin kananan yara mata, mai shekara 7 da kuma mai shekara 9.

Kara karanta wannan

2022: Kano ta ware miliyan N800 domin magance talauci da rashin aiki a tsakanin mata

Shari'a a Kotu
Abun Mamaki: An kama mahaifi da abokinsa dumu-dumu suna lalata da 'yayansu mata biyu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Tun Yaushe suke aikata wannan ta'adi?

Kazalika kotun ta gano cewa tun a shekarar 2019, mahaifin yaran biyu da amininsa suka kulla yarjejeniya a tsakaninsu.

Bayan barazanar duka da suka wa yaran, mahaifin na tura ɗaya daga cikin yayan gidan abokinsa yana lalata da ita, shi kuma ya cigaba da aikata jima'i da ɗaya.

Kotu ta kama su da laifi

A cewar alkalin kotun:

"Aikata haka ya saba wa dokar sashe na 97 da na 287 na kundin laifuka na ƙasa da hukunci."

Sai dai a nasu ɓangaren, waɗan da ake zargi sun musanta laifukan da ake zarginsu da shi a gaban kotu.

Mai gabatar da ƙara, kuma lauyan gwamnatin jihar Gombe, Barista Hafsat Aliyu Abubakar, ta gabatar da shaidu 6 a gaban kotu domin tabbatarwa.

Kara karanta wannan

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

Bayan haka shima a bangaren shi, lauyan dake kare waɗan da ake zargi, Barista Yakubu Chidimma, ya gabatar da nashi shaidun guda biyu, waɗan da kannen mutanen da ake tuhuma ne.

Wane hukunci kotu ta yanke?

Daga karshe bayan sauraron kowane bangare, Mai Shari'a Joseph Ahmed Awak, ya yanke wa mahaifin yaran hukuncin zaman gidan kaso na shekara 17.

Yayin da shi kuma abokin nasa zai shafe shekara 10 a gidan gyaran hali, kamar yadda alkalin ya zayyana.

A wani labarin kuma Wani magidanci ya lakadawa diyarsa duka har Lahira saboda ya kasa lallashinta

Gwamnatin jihar Ogun ta damke wani mutumi da zargin ya hallaka ɗiyarsa ta cikinsa ta hanyar lakaɗa mata dukan kawo wuka, kuma ta mika shi ga rundunar yan sanda domin cigaba da bincike.

Matarsa ta bayyana cewa ta haɗa kai da mijinta wajen kashe yayansu biyu saboda talauci ya musu katutu kuma sukaɓrasa mafita.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi ruwan sama a Masar, kunamai sun addabi mutane a cikin gidajensu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262