Innalillahi: Allah ya yi wa mahaifin jarumi Umar Faruk Gombe rasuwa
- Jarumi Umar Faruk Gombe ya yi babban rashi na mahaifinsa, Alhaji Sani Labaran a garin Gombe da ke arewacin Najeriya
- Kamar yadda abokan sana'ar jarumin suka dinga wallafawa a shafukansu na Instagram, za a yi jana'izarsa da karfe goma na safiyar Laraba
- Ba a nan abokan sana'arsa suka tsaya ba, sun yi masa fatan samun rahama yayin da za a yi jana'izar a fadar sarkin Gombe
Allah Ya yi wa Alhaji Sani Labaran, mahaifin jarumi Umar Faruk Gombe rasuwa a yammacin ranar Talata kamar yadda abokan sana'arsa na Kannywood suka wallafa a shafukansu.
Kamar yadda wallafar Salisu S. Fulani ta nuna, za a yi jana'izar dattijon a ranar Laraba wurin karfe goma na safe a fadar sarkin Gombe da ke jihar Gombe.
Kamar yadda sanarwar ta kara, ta yi wa marigayin addu'ar samun rahamar Ubangiji da samun aljanna a matsayin makomarsa.
Gawar Sani Dangote za ta iso Kano daga Amurka a yau Talata domin jana'iza
A wani labari na daban, a yau Talata ake sa ran gawar Sani Dangote, kanin mashahurin mai arzikin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, za ta iso Najeriya daga kasar Amurka inda ya rasu.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Sani shi ne mataimakin shugaban kamfanonin Dangote kuma ya rasu a ranar Lahadi a Amurka bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Wata majiya makusanciya ga iyalan ta ce, "Sani Dangote tuni dama ya ke fama da sankarar hanji kuma ya tafi Amurka domin samun magani, amma kamar yadda Allah ya so, ya rasu ya na da shekaru 61.
"Babu shakka, iyalan Dangote sun matukar jin mutuwar nan, amma mun karba wannan rashin tare da fawwalawa Allah mai girma lamurranmu."
Asali: Legit.ng