Boko Haram Sun Saka Karfin Tattalin Arzikin Arewa Maso Gabas Ya Ragu Da Kashi 50, Bankin Duniya
- A wani sabon rahoto da aka samu daga bankin duniya, an gano cewa ayyukan ‘yan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya sun ja tabarbarewar tattalin arziki da 50%
- Rahoto daga yankin tafkin Chadi, Adamawa, Borno da Yobe an gano yadda tsakanin shekarar 2009 zuwa 2013, harkokin tattalin arziki daga kaso 10 zuwa 14 bisa 100
- Har ila yau rahoton ya nuna saukar tattalin arziki daga 2013 zuwa 2018 da kaso 50% sannan hatta noman hatsi ya ragu a bangarorin da ke da rashin tsaro
Wani sabon rahoto daga bankin duniya ya bayyana yadda harkokin ‘yan Boko Haram su ka yi sanadin tabarbarewar harkokin tattalin arziki da kashi 50 cikin 100, 21 Century Chronicle ta ruwaito.
A rahoton, an samu tabarbarewar arziki a bangaren tafkin Chadi, Adamawa, Borno da Yobe, an gano cewa tsakanin 2009 zuwa 2013 tattalin arziki ya ragu da kaso 10 zuwa 12 sannan zuwa 2018 ya ragu da 50%.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Matsalar Boko Haram kadai ta isa talauta yanki
Masana harkokin tattalin arziki, bankin duniya da marubucin rahoton, Mr. Marco Hernandez sun bayyana cewa:
“A arewacin Najeriya, mun ga yadda noman hatsi ya ragu da fiye da 50% sakamakon rikicin rashin tsaro.
“Idan ka kalli matsalar Boko Haram kadai banda sauran matsalolin tsaron da ke yankin zaka gane dole a samu tabarbarewar tattalin arziki a yankin.”
Hernandez ya kula da yadda Boko Haram ya kawo matsaloli ga makwabtan jihohin da matsalar ke addaba inda yanzu ma har kai musu farmaki ake yi.
Bankin ya yi nuni da cewa matsawar ana son yankin ya daukaka, wajibi ne a kawo gyara ga hanyoyi don mutane su dinga kai komo da kayan kasuwanci, da kuma matsalar rashin shugabanci mai kyau da ma’adanai.
Darektan Bankin duniya na Najeriya, Shubhan Chaudhuri a wani tsokaci da ya yi, ya yi kira ga kasar nan da ta yi gaggawar kawo karshen rashin tsaro a kasar nan don kawo ci gaba musamman a arewa maso gabas.
Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna
A baya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.
A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.
Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.
Asali: Legit.ng