Hotunan Sheikh Ahmad Gumi yayinda ya ziyarci garin Fulanin da ya ginawa Makaranta

Hotunan Sheikh Ahmad Gumi yayinda ya ziyarci garin Fulanin da ya ginawa Makaranta

  • Babban Malamin addinin Musulunci ya ziyarci makaranta da asibitin da yake ginawa Fulani a jihar Kaduna
  • Rahotanni sun gabata cewa Sheikh Gumi ya ginawa wasu Fulani makaranta domin ilmantar da su
  • Gumi ya ce a ra'ayinsa, hanyar rage yan bindiga da masu garkuwa cikin Fulani shine ilmantar da su

Kaduna - Shahrarren Malamin Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Mahmoud Gumi, ya ziyarci garin Fulanin da yake ginawa makaranta da asibiti a jihar Kaduna.

Malamin wanda ya bayyana hotunan ziyarar a shafinsa na Facebook ya bayyana cewa ziyarar ganin ido ya kai tare da tawagarsa.

Hadiminsa, Salisu Webmaster ya bayyana haka.

Hotunan sun bayyana yadda Malamin ya yi jawabi da wa'azi ga mata da yawa cikinsu har da wadanda ba Musulmai ba.

Jawabin yace:

"Sheikh Ahmad Gumi wurin gani da ido na makarantar da Asibitin da yake ginawa al'ummar Fulani domin ilmantar da su a Janjala, karamar hukumar Kagarko dake Kaduna.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya samo mafita ga lamarin 'yan bindiga, ya bude wa Fulani makaranta

Wannan ziyarar gani da ido da Malam yayi da tawagarsa yayi ta ne a ranar Lahadi 14/11/2021."

Kalli hotunan:

Hotunan Sheikh Ahmad Gumi
Hotunan Sheikh Ahmad Gumi yayinda ya ziyarci garin Fulanin da ya ginawa Makaranta Hotuna: Ibrahim Isa
Asali: Facebook

Hotunan Sheikh Ahmad Gumi
Hotunan Sheikh Ahmad Gumi yayinda ya ziyarci garin Fulanin da ya ginawa Makaranta Hotuna: Ibrahim Isa
Asali: Facebook

Hotunan Sheikh Ahmad Gumi
Hotunan Sheikh Ahmad Gumi yayinda ya ziyarci garin Fulanin da ya ginawa Makaranta Hotuna: Ibrahim Isa
Asali: Facebook

Sheikh Gumi ya samo mafita ga lamarin 'yan bindiga, ya bude wa Fulani makaranta

Sheikh (Dr.) Ahmad Gumi ya kafa makarantar makiyaya a cikin dajin Kaduna, inda ya dage cewa samar da ababen more rayuwa ga makiyaya a lungu da sakonsu zai taimaka wajen dakile munanan akidunsu.

Shehin malamin ya musanta batun cewarsa Najeriya ta zo karshe idan aka ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, inda ya kara da cewa ana yi masa kuskuren fahimta.

Ya ce rashin tsaro a Najeriya, musamman lamarin ‘yan bindiga zai zama tarihi, domin ‘yan bindiga a shirye suke su yi watsi da makamansu idan aka samar musu da damammaki na ilimi da sauran ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

An shigar da Hafsat Barauniya kotu kan amsar kudi amma taki yin aikin

Ya sanya wa makarantar suna Sheikh Uthman Bin Fodio Centre, wacce ke dajin kiwo na Kagarko, kusa da Kauyen Kohoto a Jihar Kaduna.

Jaridar Vanguard ta ruwaito malamin na cewa:

"Idan cibiyar wacce aka tsara don ilimantar da makiyaya ta kasance kamar kowacce a cikin kasar, 'yan Najeriya za su zauna lafiya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng