Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

Wasu matasan 'yan Najeriya sun nuna wa duniya cewa ana iya damawa da su a kowani yanayi, kuma a shirye suke su shiga a fafata da su a duniyar kera motoci.

Duk da tarin kalubale da suka fuskanta ta fuskacin kudi, kayan aiki da tallafi daga hukumomi, matasan sun kera motocin da ya ja hankalin mutane da yawa.

A wannan zaure, Legit.ng za ta waiwayi wasu matasan yan Najeriya uku da suka nunawa duniya hazikancinsu a bangaren kere-kere.

1. Jerry Isaac Mallo

Matashin ya ja hankali a kafofin watsa labarai sosai a shekarar 2019 lokacin da ya kera wata motar gudu daga kayayyakin da aka yi su da sinadarin 'carbon'. A cewarsa, sai da ya siyar da wayarsa lokacin da yake bukatar kudi.

A yayin gwada motar a 2019, mutane da dama sun kewaye shi. An yi gagarumin bikin kaddamar da motar ne domin abun ya birge mutane sosai.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi ruwan sama a Masar, kunamai sun addabi mutane a cikin gidajensu

2. Dalibin ajin karshe na FUTMINNA

Wani bidiyo ya shahara game da wani dalibin jami'ar tarayya ta Minna (FUTMINNA) wanda ya kera wata mota mai kama da Escalade a zaman aikin kammala karatunsa.

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu
Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

A dan gajeren bidiyon, an gano dalibin tare da abokansa suna tura motar a cikin makarantar yayin da mutane suka cika da al'ajabi.

3. Ibitoye Olajide Micheal

A yan kwanaki da suka gabata, Ojajide ya sanya mutane tofa albarkacin bakunansu lokacin da ya bayyana cewa sai da ya shafe tsawon shekaru hudu don kawai ya kera wata motar gudu.

Matashin ya kara da cewa saboda rashin mataimaki, ya dauki nauyin aikin ne daga dan kudade da yake tarawa na alawus dinsa na hidimar kasa.

Abokai uku sun kera mota mai tafiya a kan ruwa ta hanyar amfani da kayan gida, bidiyon ya birge mutane da yawa

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wani mutum ya hargitsa zaman lafiyar banki kan batun BVN

A wani labarin, mun kawo a baya cewa abokai uku sun baje kolin motocin da suka kera mai ban mamaki.

Mutanen da ba a san ko su wanene ba, a cewar TRT World sun kirkiri motocin da ke tafiya a kan ruwa da kansu.

Legit.ng ta tattaro cewa motar anyi ta ne ta hanyar amfani da kayan gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng