Bamu yarda da Farfesancin Isa Pantami ba, Uwar Kungiyar Malaman Jami'a ASUU

Bamu yarda da Farfesancin Isa Pantami ba, Uwar Kungiyar Malaman Jami'a ASUU

  • Kungiyar ASUU ta yi watsi da nadin Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, matsayin Farfesa da Jami'ar Fasaha ta Owerri FUTO tayi
  • Wannan ya shiga jerin wadanda suka caccaki jami'ar FUTO kan nadin Ministan matsayin cikakken Farfesa
  • ASUU ta ayyana wasu jerin tambayoyi da take bukatar amsoshinsu kafin a amince da nadin Pantami

Abuja - Kungiyar Malaman Jami'o'in Najeriya ASUU ta yi watsi da rahoton wani kwamiti da sashenta na Owerri tayi kan nadin Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, matsayin Farfesa da Jami'ar Fasaha ta Owerri FUTO tayi.

Shugaban Kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa akwai kura kan Farfesancin Malam Isa Ibrahim Pantami.

Ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai ranar Litnin a Abuja, bayan ganawar kwana biyu da kwamitin zantarwar ASUU tayi, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Kano ta yi cikar kwari yayin da mataimakin gwamna ya aurar da ‘yarsa

Yace jama'a su saurari sakamakon binciken kwamitin da ta nada don gudanar da bincike kan lamarin.

Yace:

"Yan majalisar zartaswar NEC ta ASUU, kamar sauran yan Najeriya bata yarda da rahoton ASUU FUTO ba. Akwai shakku da kura iri-iri kan cancantar Dr. Isa Ali Ibrahim (Pantami) na zama Farfesa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Rahoton FUTO ya gaza bayani da hujja kan nadin Pantami matsayin Farfesa bisa gogewa da dadewa a aiki, da kuma tarihinsu a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU).”

ASUU ta yi kira ga shugabannin jami'o'in Najeriya da wasu manyan makarantu su bada hadin kai wajen kare mutuncin sashen Ilimin Najeriya.

Uwar Kungiyar Malaman Jami'a ASUU
Bamu yarda da Farfesancin Isa Pantami ba, Uwar Kungiyar Malaman Jami'a ASUU Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Akwai tambayoyi da dama kan cancantar Pantami

ASUU tace duk da cewa kwamitin sashen FUTO ta amince da nadin Pantami matsayin Farfesa, Sakataren kwamitin da kansa yayi amai ya lashe inda yace shi fa bai amince da rahoton ba.

Kara karanta wannan

Hotuna da sunayen jaruman Sojojin da aka kashe a artabu da yan ta'adan ISWAP

Kungiyar tace zata gudanar da bincike kan lamarin.

Mr Osodeke yace:

"Akwai tambayoyi daban-daban kan: Shin Dr. Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya cika sharadin shekaru 12 kamar yadda aka bayyana cikin takardar talla? Shin yana da wallafe-wallafen da ake bukata kuma kashi 70% na yanar gizo? Shin Minista dake ofishin Gwamnatin tarayya zai iya karban wani aiki a jami'a? Shin zai iya ayyukansa matsayin Minista kuma Farfesa duk lokaci guda?"
"Shin Dr. Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya cika sharrudan karantarwa, horar da dalibai, da kwarewa da ake bukata ga Farfesa?"

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng