ISWAP sun tilasta wa manoman kauyukan Borno biyan haraji, sun ce zakkar gona ce

ISWAP sun tilasta wa manoman kauyukan Borno biyan haraji, sun ce zakkar gona ce

  • Mazauna wasu kauyukan da ke jihar Borno sun koka kan yadda 'yan ta'adda ke tilasta musu biyan haraji ko kuma karbar amfanin gona a matsayin zakka
  • Mazauna Damboa sun bada labarin salon 'yan ta'addan wurin amfani da karfi da yaji domin kwace musu amfanin gonakinsu da dabbobin da suka kiwata
  • Tun farko a kan yi yarjejeniya da 'yan ta'addan cewa, za su bar su su yi noma amma ya zama tilas su bayar da zakkar matukar suka girbe amfani

Borno - Jama'a masu zama wasu daga cikin kauyukan Borno sun koka da halin da suka samu kansu na tilascin biyan haraji da 'yan ta'adda suka saka musu a cikin zakkar amfanin gona.

Kamar yadda BBC ta wallafa, jama'a mazauna garin Damboa sun sanar da yadda 'yan ta'addan ke amfani da karfi wurin kwace amfanin gona da dabbobi, kuma biyayya a gare su ta zama dole domin tsira.

Kara karanta wannan

Da duminsa: ISWAP sun sake kai hari, suna luguden wuta a Borno da kone gidaje

ISWAP sun tilasta wa manoman kauyukan Borno biyan haraji, sun ce zakkar gona ce
ISWAP sun tilasta wa manoman kauyukan Borno biyan haraji, sun ce zakkar gona ce. Hoto daga BBC.com
Asali: UGC

Wannan al'amarin ya kara fitowa ne a lokacin da ake cigaba da rade-radin cewa 'yan ta'addan ISWAP na amshe haraji daga wurin makiyaya da manoman jihar Borno.

'Yan ta'addan kan ba manoma damar cigaba da ayyukan gonakinsu a kan sharadin cewa za su bada haraji ko zakka idan sun girbe amfaninsu, BBC ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Garin Damboa da ke jihar Borno ya na da kusanci da na Chibok, yankunan da ke fama da miyagun hare-haren 'yan ta'addan.

ISWAP sun sake kai hari, suna luguden wuta a Borno da kone gidaje

A wani labari na daban, wasu mayaka da ake zargin ‘yan ISWAP ne yanzu haka suna kai farmaki karamar hukumar Askira Uba da ke jihar Borno.

An samu rahotanni a kan yadda suka babbaka gidaje a kauyen Dille da ke karamar hukumar a wani hari da su ka kai kwanakin karshen mako, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Borno: Arangama ta da 'yan ta'addan ISWAP a kan titi, Malamin makaranta

Majiyoyi daban-daban sun shaida wa Daily Trust yadda ‘yan ta’addan suka kai farmaki kauyen da misalin karfe 5:30pm. Majiyar ta shaida yadda suka balle shaguna sannan suka tsere da kayan abincin tare da kwasar na gidaje.

Har yanzu dai ba a kammala bayar da rahoto akan yawan mutane da gidajen da lamarin ya shafa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng