Borno: Hotunan ragargazar da sojoji suka yi wa ISWAP a Askira Uba, sun kashe 50 sun kwato makamai
- Rundunar Operation Hadin Kai ta ragargaji mayakan ISWAP 50 sannan ta lalata musu makamansu da ke sansaninsu a karamar hukumar Askira Uba da ke jihar Borno
- Idan ba a manta ba bataliyar 115 Task Force ta yi karon batta da mayakan ISWAP a ranar 13 ga watan Nuwamban 2021 a Askira Uba
- Sai dai sakamakon turnukun, mayakan ISWAP sun halaka kwamandan 28 Task Force tare da wasu sojoji 3 har lahira, wanda hakan ya matukar harzuka sojoji
Jihar Borno - Rundunar Operation Hadin Kai ta Sojoin Nigeria da ke arewa maso gabas ta samu nasarar halaka mayakan ISWAP guda 50 a karamar hukumar Askira Uba.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta shafin su na Facebook sun bayyana yadda sojojin su ka yi gaba da gaba da mayakan ISWAP wanda har lalata mu su kayan yakin su suka yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Lamarin ya auku ne a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba inda jaruman sojin suka samu nasarar halaka manya da kananun mayakan kungiyar.
Dama mayakan sun halaka wasu sojoji a makwan da ya gabata
Idan ba a manta ba, bataliya ta 115 Task Force ta yi karon batta da mayakan ISWAP a karamar hukumar Askira Uba a ranar 13 ga watan Nusamban 2021.
Yayin da sojojin su ke kokarin kare sansanin su, mayakan sun halaka kwamandan runduna ta 28 Task Force tare da wasu sojoji 3.
Yayin da fadan ya kara nisa, rundunar OPHK na sama sun harbi mayakan a kauyen Leho da ke karamar hukumar Askira Uba.
Kuma sun tabbatar sun halaka mayakan ISWAP din da dama tare da lalata musu kayan yakinsu.
Da Duminsa: ISWAP ta ƙaryata Rundunar Sojojin Nigeria, ta bayyana adadin sojojin da ta kashe a harin Askira
Cikin kayan yakinsu da sojojin su ka lalata akwai motar yakinsu ta MRAP da wasu motocin yaki 11. Sannan sojin sun samu bindigogi kirar AK 47 guda 5 da sauran miyagun makamai.
Runduna ta 115 Task Force ta samu damar bincike kauyen Leho da kewaye, inda su ka ga gawawwakin mayakan ISWAP 3, 2,560 rounds ba 7.62 special da 29 rounds na 7.62mm NATO ammunition da mayakan su ka tsere su ka bari.
Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna
A baya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.
A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.
Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.
Asali: Legit.ng