Dan uwan Hamshakin Attajiri a nahiyar Afirka, Aliko Dangote, ya rigamu gidan gaskiya

Dan uwan Hamshakin Attajiri a nahiyar Afirka, Aliko Dangote, ya rigamu gidan gaskiya

  • Mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote Group, Sani Dangote, ya riga mu gidan gaskiya
  • Rahotanni sun bayyana cewa Sani Dangote ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya a kasar Amurka ranar Lahadi
  • Kafin rasuwarsa, Sani ya zuba hannun jari a ɓangarorin da dama na kamfanin su, sannan kuma ya rike mukamai da kamfanin

Kano - Mataimakin shugaban kamfanin Dangode Group kuma ɗan uwa ga Attajirin Afirka, Aliko Dangode, Sani Dangote, ya riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun bayyana cewa Sani Dangote ya rasa rayuwarsa ne bayan fama da jinya a kasar Amurka ranar Lahadi.

Wannan na kunshe ne a wani gajeren sako da rukunin kamfanonin Dangote, Dangote Industries, suka buga a shafinsu na Facebook.

Sani Dangote
Dan uwan Hamshakin Attajiri a nahiyar Afirka, Aliko Dangote, ya rigamu gidan gaskiya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sakon yace:

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Allah ya yi wa ƙanin Aliko Dangote rasuwa

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, cikin raunanniyar zuciya da kuma miƙa lamari ga Allah (SWT), muna sanar da rasuwar mataimakin shugaban mu, Alhaji Sani Dangote, a yau 14 ga watan Nuwamba 2021."
"Muna rokon Ubangiji Allah mai girma da ɗaukaka ya gafarta masa, ya kuma saka shi a gidan Aljannatul Firdaus maɗaukakiya."

Waye Sani Dangote?

Kafin rasuwarsa, Sani Dangote ya zuba hannun jari a masana'antun sarrrafa abubuwa, banki, noma da kiwo da kuma harkokin mai.

Hakanan kuma ya shiga majalisar gudanarwa ta kamfanonin su da dama, da suka haɗa da, Nigerian Textile Mills, Nutra Sweet Limited, Gum Arabic Limited, Dangote Textile Mills Limited.

Sauran sun haɗa da Alsan Insurance Brokers, kamfanin Dan-Hydro Limited, kamfanin Dansa Food Processing Limited da kuma Dangote Farms Limited.

A wani labarin kuma Sojojin Najeriya sun hallaka kasurgumin kwamandan yan ta'adda da wasu 37 a Askira

Rahoto ya nuna cewa sojojin sun shirya sun sake farmakan yan ta'addan domin ɗaukar fansa kan kisan manyan sojoji.

Kara karanta wannan

Har bayan wata 7, an kasa sasanta rikicin Kwankwaso da Wali a PDP

Mazauna garin Askira Uba sun yaba da yadda dakarun sojin suka ɗauki matakin gaggawa yayin da yan ISWAP suka shigo kauyen su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262