Yadda Buhari yake kashe makudan biliyoyi wajen sayen motoci, yana laftowa Najeriya bashi

Yadda Buhari yake kashe makudan biliyoyi wajen sayen motoci, yana laftowa Najeriya bashi

  • Gwamnatin Tarayya tana cigaba da batar da kudi wajen abubuwan da ba su zama mata larura ba
  • A daidai wannan lokaci kuma Shugaba Muhammadu Buhari yana kiran a rage facaka da dukiya
  • Duk da Najeriya ta dogara da bashi sosai, an sake ware Naira biliyan 1.6 domin sayen motoci a 2022

Abuja - Wani rahoto da jaridar Premium Times ta fitar a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba, 2021, ya zargi gwamnatin tarayya da kin rage facakar dukiya.

A daidai lokacin da gwamnatin Najeriya take cin bashi duk shekara, ta ki daukar mataki domin rage adadin kudin da ta ke kashewa na babu gaira-babu dalili.

Shugaba Muhammadu Buhari yana da’awar a rage facaka, amma kasafin kudin gwamnatinsa sam bai nuna Najeriya da gaske take yi wajen rage almubazzaranci ba.

Kara karanta wannan

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

Sama da N1.6bn za su kare a kan motoci

Fadar shugaban kasa za ta kashe Naira biliyan 1.6 wajen sayen sababbin motoci a 2022. Hakan na zuwa ne shekara guda bayan an saye motocin kusan N500m.

Baya ga kudin da shugaban kasa zai kashe a kan sayen motoci, an warewa mataimakin shugaban kasa Naira miliyan 30 domin samun sababbin motocin hawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga lokacin da jam'iyyar APC ta hau mulki, an kashe Naira biliyan biyar a sayen motoci. Jaridar tace wadannan kudi sun isa a gina dakunan shan magani 500.

Yadda Buhari yake yawo
Motocin Buhari yayin kamfe a Kwara Hoto: www.thebridgenewsng.com
Asali: UGC

Idan da an maida hankali kan kiwon lafiya, da wannan kudi, kowace jiha za ta samu asibiti akalla 13.

Ana yin wannan ne duk bashi, maimakon ayi watsi da abubuwan da ba su zama dole ba. Wannan ya sa irinsu Eze Onyekpere ke kokarin hana irin wannan facaka.

Kara karanta wannan

Majalisa ta kawo dabarar hana magudin zabe, za a rika aiki da na’ura wajen tattara kuri’u

Bashi yana ta karuwa a kan Najeriya

Kasafin da gwamnatin tarayya tayi na shekarar 2022 mai zuwa yana kunshe da gibin sama da Naira tiriliyan shida, hakan na nufin sai an hada da cin bashi.

Yawan bashin da ke wuyan Najeriya ya karu sosai bayan Buhari ya hau mulki. A gwamnatin APC ne bashin da ake bin Najeriya a ketare ya nunku fiye da sau uku.

Gwamnati ta kashe kudi a cefanen abinci da man jirgin shugaban kasa, sama da abin da aka warewa lafiya, a lokacin da Ministar tattali take kukan babu kudi.

Jam'iyyar APC tayi hankali - Kawu Sumaila

A ranar Lahadin nan aka ji Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila ya yi amfani da Facebook, ya yi fashin baki a kan halin da siyasar Najeriya take ciki a halin yau.

Kawu Sumaila yace APC ta dandana kudarsa a zaben jihar Anambra, sannan yace yana tausayin ranar da za a ce jam’iyyar APC ba ta rike da kujerar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Hukumar kwastam ta tattarowa Gwamnati Naira Biliyan 86 a tashar Apapa a kwana 30

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng