Rundunar sojin Najeriya ta magantu kan jita-jitar shirin yiwa Buhari juyin mulki

Rundunar sojin Najeriya ta magantu kan jita-jitar shirin yiwa Buhari juyin mulki

  • Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta yi mai yiyuwa ta kowane hali a yunkurin jawo sunanta cikin harkokin siyasar cikin gida
  • Sojoji na mayar da martani ne ga wani labari da wani shafin yada labarai na intanet ya wallafa yana mai cewa tana yunkurin juyin mulki a Najeriya.
  • Kakakin rundunar, Birgediya-Janar Bernard Onyeuko ya ce rahoton karya ne kuma aiki ne na masu tada fitina a kasar

Rundunar sojin Najeriya ta yi watsi da wani rahoton da wasu kafafen yada labarai suka wallafa na cewa ana shirin juyin mulki a Najeriya.

Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan watsa labarai na tsaro, Birgediya-Janar Bernard Onyeuko ya aikewa majiyar Legit.ng a ranar Lahadi, 14 ga watan Nuwamba.

Sojojin Najeriya sun magantu kan jita-jitar za su yiwa Buhari juyin mulki
Birgediya-Janar Bernard Onyeuko | punchng.com
Asali: UGC

Wani bangare na sanarwar ya karanta cewa:

Kara karanta wannan

Borno: Yadda samamen sojoji a sansanin ISWAP ya janyo halakar sojoji

“An jawo hankalin hedikwatar tsaro a kan wata karya da wata jarida ta yanar gizo ta Naija News House ta buga kan sojojin Najeriya da ke gargadin ‘yan siyasa da jami’ai kan juyin mulkin da ta ta'allaka da Birgediya Janar Onyema Nwachukwu - mai magana da yawun rundunar soji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Rubutun aiki ne na masu yin barna kuma makiya kasa. Kokari ne da gangan da kididdiga don yaudarar jama'a da nufin haifar da rashin jituwa a cikin harkokin siyasa."

Hakazalika, jami'in ya bayyana cewa, rundunar soja bata da alaka da siyasa ko hannu a wani bangaren siyasa, don haka 'yan Najeriya su guji rahoton gidan jaridar.

Lamari ya yi zafi, dattawan Arewa sun zauna don neman mafita ga matsalolin Arewa

A wani labarin, kungiyar farfado da martabar Arewa (NRO) a ranar Lahadi ta tattaro masu ruwa da tsaki da dattawan yankin Arewa domin tattauna kalubalen yankin Arewa a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kashe mayakan ISWAP da yawa yayin da artabunsu da sojoji ya shiga awa na 8

Taron yana daga cikin kokarin suke yi na magance matsalolin da ke kara ta'azzara a yankin da yanzu haka ke karuwa cikin wani yanayi mai ban tsoro, Daily Trust ta ruwaito.

Yana daga cikin aikin kungiyar na maido da jituwa, dauwamammen zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki da maido da halayya da mutunci ga mutumci da asalin Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.