SSS sun kame matashin da ya zolayi Zainab Nasir kan auren 'yar gwagwarmaya Malala
- Hukumar SSS ta kame wani matashi da ya zolayi wata matashiya 'yar gwagwarmaya a kafar Facebook
- Matashiyar ta yi ikrarin daure matashin yayin da ya yada wani hoton da wasu maganganu da basu mata dadi ba
- Sai dai, jim kadan bayan rahoton kame shi, an ga matashin ya yi wani rubutu a shafinsa na kafar Facebook
Kano - Hukumar tsaron farin kaya ta SSS a Kano ta kama wani mai amfani da kafar Facebook, Ibrahim Sarki Abdullahi, da laifin zolayar wata mai fafutukar kare hakkin mata, Zainab Nasir kan auren 'yar fafatuka Malala.
Wata majiya a ofishin hukumar ta Kano ta tabbatar wa Daily Nigerian kama Mista Abdullahi, inda ta ce ana yi masa tambayoyi ne saboda taba mutuncin Zainab.
A baya dai Zainab ta bayyana ra'ayin cewa "aure ba nasara ba ne", kuma hakan ya haifar da cece-kuce a kafar Facebook, lamarin da yasa ta shahara.
Abdullahi ya zolayi Zainab ne a ranar da Malala Yousafzai ta bayyana auren ta ga duniya, wanda hakan ya haifar da rudani duba da ra'ayin Malala kan batun sukar aure.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Maganganun Abdullahi sun danganta Zainab da Malala ne ganin suna da ra'ayi iri daya, a hasashen Abdullahi.
A cikin rubutunsa, Abdullahi ya sanya hoton Zainab tare da zolayar da cewa "Malala ta shushe mu".
Daga nan Zainab tace ba za ta amince ba sai ta dauki matakin doka bayan shawarwari.
Sai dai, jim kadan rahoton kame Abdullahi da yi masa tambayoyi, an ga rubutu a kan shafinsa na Facebook, inda ya ce:
"SalamuAlaykum."
Legit.ng Hausa ta bibiyi rubutun, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai yi karin bayani an sako shi ko musanta kamun ba.
Hakazalika, mabiyansa a shafin Facebook sun yi ta tambayoyi kan batun.
Bidiyon yadda wani mutum ya hargitsa zaman lafiyar banki kan batun BVN
A wani labarin, watakila ya gaji da hidimar su, wani dan Najeriya ya kutsa kai bankinsa domin ya bayyana ra’ayinsa na yanke hulda da su.
Mutumin da ya fusata ya hargitsa lamurra yayin da ya yi ihu da babbar murya cewa a rufe asusunsa.
A cikin wani dan gajeren bidiyon da @instablog9ja ya yada a Instagram, ana iya jin mutumin yana gunaguni game da batun BVN kuma ya fusata da kururuwa tare da cewa 'aikin banza'.
Asali: Legit.ng