Kano: 'Yan sanda sun ceto tsoho mai shekaru 80 daga hannun masu garkuwa da mutane

Kano: 'Yan sanda sun ceto tsoho mai shekaru 80 daga hannun masu garkuwa da mutane

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ceto wani tsoho mai shekaru tamanin mai suna Alhaji Nadabo daga hannun miyagu
  • Masu garkuwa da mutanen sun sace tsohon a garin Chiromawa da ke karamar hukumar Garun Malam ta jihar Kano
  • Sai dai kwamishinan 'yan sandan ya aike jami'ai inda suka hada kai da jama'ar yankin tare da 'yan sintiri wurin ceto shi

Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta ceto wani tsoho mai shekaru tamanin mai suna Alhaji Nadabo, wanda aka sace a garin Chiromawa da ke karamar hukumar Garun Malam ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan ga manema labarai kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin daukar fansa, sun kashe wasu matan aure tare da kone gidaje a Taraba

Kano: 'Yan sanda sun ceto tsoho mai shekaru 80 daga hannun masu garkuwa da mutane
Kano: 'Yan sanda sun ceto tsoho mai shekaru 80 daga hannun masu garkuwa da mutane. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce bayan samun rahoton cewa an sace tsohon, rundunar sun dauka matakin gaggawa.

Ya ce, "Bayan samun rahoton, kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Sama'ila Shu'aibu Dikko, ya tada tare da umartar wata kungiyar jami'an Operation Puff Adder wadanda suka samu shugabancin CSP Usman Maisoro domin ceto tsohon tare da kamo masu laifin."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta ruwaito cewa, kamar yadda yace, bayan 'yan sanda sun matsanta wa masu garkuwa da mutanen, sun sako wanda suka sace.

"Da kokarin 'yan sintiri da na jama'ar yankin, an gano inda masu garkuwa da mutanen suke kuma an tsananta bibiyarsu. Sun sako wanda suka sace ba tare da cutar da shi ba a ranar sannan suka tsere."
"An sake tura jami'an Puff Adder wurin kuma an umarcesu da su tabbatar da sun kama miyagun," Kiyawa yace.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13

Kano Tumbin Giwa: Ganduje ya dauki masu rawar koroso 45 aikin dindindin

A wani labari na daban, a ranar Laraba da ta gabata, gwamnatin jihar Kano ta mika takardun daukar aikin dindindin ga masu rawar gargajiya wadanda aka fi sani da 'yan rawan koroso 45 a jihar.

Sabbin ma'aikatan rawan da aka dauka aiki an saka su a matsayin kananan ma'aikata ne wadanda za su yi aiki karkashin ma'aikatar tarihi da ofishin al'adu na jihar.

A yayin mika takardun daukar aikin a ma'aikatar, kwamishinan ma'aikatar al'adu, Ibrahim Ahmad Karaye, ya yi bayanin cewa wannan kyautatawar an yi ta ne domin karrama kananan ma'aikata masu aiki tukuru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng