Harin ISWAP a Borno: Abubuwan da ya kamata ku sani game da Janar din aka kashe

Harin ISWAP a Borno: Abubuwan da ya kamata ku sani game da Janar din aka kashe

  • A jiya ne aka samu labarin mutuwar wani babban jami'in soja a yakin da ake da ta'addanci a Arewa maso gabas
  • An kashe jami'in ne a yayin da wasu 'yan ta'addan ISWAP suka kai hari wani sansanin soja a jihar Borno
  • Tare dashi, an hallaka wasu jami'an soja duk da cewa an kashe wasu 'yan ta'addan ISWAP din da yawa

A jiya ne muka samu rahotannin dake cewa Brig-Gen. Dzarma Zirkusu ya rigamu gidan gaskiya yayin da yake jagorantar jami'ansa a fagen daga lokacin da 'yan ISWAP suka kai musu hari.

Kafin mutuwarsa, ya rike mukamai da yawa a gidan soja, Daily Trust ta ruwaito.

Babban jami'in soja da ISWAP ta kashe | Hoto: bbc.com
Harin ISWAP a Borno: Abubuwan da ya kamata ku sani game da Janar din aka kashe
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta tattaro bayanai masu muhimmanci da ya kamata ku sani game wannan jami'in.

  1. Marigayin dan asalin jihar Adamawa ne.
  2. A watan Janairu, an dauke shi daga hedkwatar sojoji ta 1, Gusau, Jihar Zamfara zuwa hedikwatar 28 Task Force Brigade dake Chibok, Jihar Borno, a matsayin Kwamanda
  3. Chibok ita ce wurin aikinsa na karshe kafin a kashe shi tare da wasu jami'ai.
  4. Marigayin shi ne babban jami’in da ya mutu a yakin da ake da ta’addanci

Kara karanta wannan

Borno: Yadda samamen sojoji a sansanin ISWAP ya janyo halakar sojoji

Borno: Yadda samamen sojoji a sansanin ISWAP ya janyo halakar sojoji

A wani labarin, samamen da rundunar sojin Najeriya ta kai wa mayakan ISWAP har sansanin 'yan ta'addan ya janyo kisan Birgediya Janar Dzarma Zirkusu da wasu sojoji uku, majiyoyi masu karfi suka sanar da Daily Trust.

Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace sojojin sun halaka 'yan ta'addan ISWAP yayin arangamar.

Ya ce baya ga kashe 'yan ta'addan, dakarun sojin sun tarwatsa motocin yakinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.