Harajin jihohi a 2021: Jerin jihohi 10 da suka samar da kudin shiga mafi karanci a Najeriya
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) kwanan nan ta buga rahoton Harajin Cikin Gida (IGR) a matakin Jiha na Rabin Shekarar 2021.
Rahoton da hukumar ta NBS ta wallafa a shafinta na yanar gizo ya bayyana cewa, daukacin jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja na da jimillar IGR na naira biliyan 849.1 a tsawon lokacin da ake nazari a kai.
Yayin da wasu jihohi suka samar da IGR mai tsoka, wasu suna da Legit.ng ta gano a jadawalin sun samar kudade kadan, lamarin da ya nuna karancin kudaden shiga na cikin gida a jihohin.
Ga 10 daga cikin jihohin Najeriya 36 da babban birnin tarayya, wadanda suke da mafi karancin kudin shiga:
- Jihar Yobe - N4.0bn
- Jihar Taraba - N4.8bn
- Jihar Gombe - N5.4bn
- Jihar Adamawa - N6.1bn
- Jihar Bayelsa - N6.4bn
- Jihar Ekiti - N6.6bn
- Jihar Benue - N6.7bn
- Jihar Kebbi - N7.3bn
- Jihar Katsina - N7.5bn
- Jihar Abia - N7.6bn
Kudaden da jihohi 36 da FCT suka samar na kudin shiga a 2021
A cikakken rahoton, Jihohi talatin da shida da babban birnin tarayya sun samar da kudi har N849.123 biliyan na kudin shiga a shekarar 2021, wanda ya bayyana cigaba fiye da na 2020 inda aka samu N612.87 biliyan.
Wani rahoton da hukumar kiyasi ta NBS ta fitar, ya bayyana cewa an samu N398 biliyan a wata ukun farkon shekarar 2021 kuma an samu N450 biliyan a wasu karin wata ukun, lamarin da ke nuna cigaba da kashi 13.21, Daily Trust ta wallafa.
Rahoton ya karkasa kudin shiga da aka samu zuwa gida biyar: Akwai PAYE, harajin kan tituna, sauran haraji, kudaden shiga daga ma'aikatu da cibiyoyi gwamnati da kuma na kai tsaye.
Asali: Legit.ng