Kasashen nahiyar Afrika 5 masu kudi mafi daraja a shekarar 2021
Mutane da dama sun san kudaden kasashen nahiyar Afrika amma ba kowa ya san darajar wadannan kudade ba idan aka kwatantasu da dalar Amurka.
Hakan ya sa Legit.ng ta kawo muku jerin kasashe 5 masu kudade mafi daraja a nahiyar Afrika kawo Nuwamba, 2021.
Ga jerinsu:
1. Dinarin Tunisiya
Wanda ke kan gaba kuma mafi karfi a nahiyar shine Dinarin kasar Tunisiya.
Shine kudi mafi daraja na biyu a nahiyar Afrika (1USD – 2.83 TND), rahoton Business Insider Africa.
2. Dinari na kasar Libya
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dinarin kasar Libya ne kudi mafi daraja a nahiyar Afrika (1 USD – 3.43 LYD).
3. Cedi na kasar Ghana
Kudin Ghana, Cedi, ya farfado bayan aiki tukuru na gwamnatin da kasar tayi, yanzu shine mai daraja na uku a Afrika (1USD – 6.07 CEDI), rahoton Africa News.
4. Dirham na kasar Maroko
Dirhamin kasar Maroko ne kudi mafi daraja na hudu a Afrika (1 USD – 9.05 Mad).
5. Pula na kasar Botswana
Kasar Botswana ce kasa ta biyar mafi kudi mai daraja a Afrika (1 USD – 11.33 Pula).
Gwamnan CBN ya gagara rike darajar Naira, Dalar Amurka ta lula zuwa N575
Farashin dala ya koma tsakanin N572 zuwa N575 a hannun ‘yan canji. Punch ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 20 a watan Satumba, 2021.
Jaridar tace dalar Amurka tana ta tashi a kasuwar canji duk da babban bankin Najeriya ya dakatar da aikin Aboki Fx da nufin a rage karyewar Naira.
Manema labarai sun ziyarci kasuwar bureau de change na ‘yan canji da ke unguwar Wuse a Abuja, inda suka ga cewa ana saida kowace Dala a Naira 574.
Rahoton yake cewa ‘yan canjin da ke Legas kuma suna saida Dala ne a kan N572. A Kano abin ya fi kamari, mutane suna sayen Dalar Amurka a kan N575.
Asali: Legit.ng