Da dumi-dumi: An kashe mayakan ISWAP da yawa yayin da artabunsu da sojoji ya shiga awa na 8

Da dumi-dumi: An kashe mayakan ISWAP da yawa yayin da artabunsu da sojoji ya shiga awa na 8

  • Dakarun sojojin Najeriya sun kashe mayakan ISWAP da yawa a artabun da suka yi a garin Askira da ke karamar hukumar Askira Uba ta jihar Borno
  • Sojojin kasa da na sama sun yi raga-raga da mayakan ta hanyar sake masu ruwan bama-bamai yayin da artabun nasu ya shiga awa na takwas
  • Sun kuma lalata motocin yakin 'yan ta'addan da dama kamar yadda kakakin rundunar sojin kasar ya bayyana

Askira Uba, jihar Borno - Wani rahoton jaridar Daily Trust ya kawo cewa an harbe mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP da dama a arangamar da suke yi da dakarun sojojin Najeriya.

‘Yan ta’addan sun kai farmaki garin Askira da ke karamar hukumar Askira Uba ta jihar Borno a safiyar ranar Asabar, 13 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun kai hari sansanin soji a Borno, suna ta musayar wuta da sojoji

Da dumi-dumi: An kashe mayakan ISWAP da yawa yayin da artabunsu da sojoji ya shiga awa na 8
Da dumi-dumi: An kashe mayakan ISWAP da yawa yayin da artabunsu da sojoji ya shiga awa na 8
Asali: Getty Images

Wata majiya ta sanar da jaridar cewa mayakan ISWAP sun kai farmakin ne da misalin karfe 9:00 na safe.

Sai dai abun bakin ciki, an rasa wani Birgediya Janar da wasu jami’ai a yayin da suke kare kasarsu amma kuma rundunar sojin kasa da na sama suna ta tayar da ‘yan ta’addan ta hanyar yi masu ruwan bama-bamai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata sanarwa da ya saki a yammacin Asabar din, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar sojin, ya tabbatar da cewar yakin na nan yana gudana.

Ya ce baya ga kisan yan ta’addan, dakarun soji na nan sun lalata manyan motocin yakinsu da dama.

Ya ce:

"Dakarun hadin gwiwa, Operation HADIN KAI na arewa maso gabas, sun kashe mayakan ISWAP da dama a arangamar da suka yi a karamar hukumar Askira Uba da ke jihar Borno.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun ragargaji dandazon mayakan ISWAP tare da sabon Wali, Sani Shuwaram

"A arangamar wanda ke gudana a har a lokacin kawo wannan rahoton, rundunar da taimakon sojin sama sun lalata A-Jet biyar, A-29 biyu, motocin yaki na Dragon biyu da motocin da akew girke bindigogi guda tara."

Hukumar Sojin Najeriya ta tabbatar da kisan Birgediya Janar a harin kwantan baunar ISWAP

Da farko mun kawo cewa hukumar Sojin Najeriya tabbatar da kisan Birgediya Janar Dzarma Zirkushu, Kwamandan rundunar 28 Task Force Brigade, dake Chibok, jihar Borno, Arewa maso gabas.

Yan ta'addan sun kashe Janar din tare da wasu jami'ansa uku, yayinda suke hanyar su ta zuwa kai dauki ga Sojoji a kauye Bungulwa dake kusa Askira Uba.

Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Onyeama Nwachukwu, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, rahoton DailyNigerian.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng