An bayyana suna Birgediya Janar da aka hallaka a harin kwantan baunan da yan ISWAP suka kaiwa Soji yau a Borno

An bayyana suna Birgediya Janar da aka hallaka a harin kwantan baunan da yan ISWAP suka kaiwa Soji yau a Borno

  • Yan ta'adan ISWAP sun kai mumunan hari sansanin Sojojin Najeriya dake jihar Borno ranar Asabar
  • Wannan ya biyo bayan kisan manyan kwamandojinsu da hukumar Soji sama tayi
  • Yayinda rundunar Birgediya Janar Dzarma Zirkushi taje kai dauki kuma, aka bude mata wuta

An bindige wani Birgediya Janar har lahira a harin kwantan baunan da yan ta'adda Daular Musulunci a yammacin Afrika ISWAP suka kaiwa jami'an Soji a jihar Borno, rahoton PRNIgeria.

Sabanin shi an hallaka jami'an Sojoji hudu a harin kwantan bautan da ya auku a Bulguma, kusa da garin Askira, a karamar hukumar Askira Uba.

Sunan Brigadier-Janar din Dzarma Zirkushi, kuma shine kwamdanda commander of 28 Task Force Brigade, Chibok.

Kun ji cewa jami'an 28 Task Force Brigade, Chibok, sun tashi daga barikinsu don kaiwa Sojin dake Askira dauki amma aka bude musu wuta.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun kai hari sansanin soji a Borno, suna ta musayar wuta da sojoji

An hallaka Birgediya Janar a harin kwantan baunan da yan ISWAP suka kaiwa Soji yau a Borno
An hallaka Birgediya Janar a harin kwantan baunan da yan ISWAP suka kaiwa Soji yau a Borno
Asali: UGC

Wani jami'in leken asiri ya bayyanaewa PRNIgeria cewa,

"Yan ta'addan ISWAP da suka kai hari Askira Uba sun lalata hatsumiyar sadarwa da bindigogi da wasu makamai dake hannunsu."
"An kashe kwamandan Soji daya a harin kwantar baunar yayinda yake jagorantar rundunar kai dauki. Hakazalika an kashe wasu Soji."
"Wasu yan ta'addan daban kuma sun kai hari kauyen Mulai, kusa da Maiduguri inda suka sace Shanu yayinda wasu suka lalata hatsumiyar sadarwa a Buni Yadi jihar Yobe kuma suka sace Janareto da magunguna."

Mun kawo muku cewa 'Yan ta'addan ISWAP sun yi musayar wuta da sojoji a wani sansanin soja da ke karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.

Wasu mazauna sun ce sun hango mayakan na ISWAP a cikin wani dogon ayarin motocin bindigu a hanyar Ngude zuwa Askira, da sanyin safiyar yau.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Daga Faransa, Shugaba Buhari ya garzaya kasar Afrika ta Kudu don halartan kasuwar baja koli

Adamu Saleh ya shaida wa The Sun cewa:

“Al’amarin ya yi muni amma ‘yan ta’addan sun janye a yanzu.”

Mazauna sun yi ikirarin cewa sun kai rahoton zirga-zirgar 'yan ta'addan ga jami'an tsaro amma ba a dauki wani mataki ba kafin wannan mummunar kungiyar ta afkawa garin Askira bayan sa'o'i.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: