Kano: Jami’an SSS sun bankaɗo ‘yan fashin da ke bin sahun mutane daga banki har zuwa gidansu
- Jami’an tsaro na fararen kaya, SSS reshen jihar Kano sun kama wasu shu’umai 3, kwararru akan bin sawun mutane zuwa bankuna don yi musu fashi da makamai bayan sun ciro kudi
- Darektan SSS na jihar, Alhassan Muhammad ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai ranar Juma’a a Kano, inda ya ce shu’uman sun kai shekaru 3 su na addabar jama’a
- A cewarsa an yi ram dasu ne bayan sun kwace babur a hannun wani mutum sannan su ka kwace N300,000 wadanda ya ciro daga banki
Jihar Kano - Hukumar tsaro ta fararen kaya, SSS ta samu nasarar damkar wasu matasa 3 da ake zargin kwararru ne wurin bin sawun jama’an zuwa bankuna don yi musu fashi.
The Nation ta ruwaito yadda Darektan SSS na jihar, Alhassan Muhammad, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da manema labarai ranar Juma’a a Kano.
Ya kara da cewa sun dade su na addabar Kano tun shekaru 3 da suka gabata.
Ya lissafo sunayen shugabannin kungiyar inda ya ce akwai Abubakar Umar mai shekaru 30, Abubakar Suleiman Mai shekaru 38 da Ya’u Abubakar mai shekaru 35.
An damke su ne bayan sun yi wani fashin
A cewarsa, an kama wadanda ake zargin ne bayan sun yi fashin babur da N300,000 daga hannun wani wadanda ya ciro a banki.
Kamar yadda ya shaida:
“Mun same su wuraren Jaen Quarters da ke Kano a wani gida bayan sun yi fashin babur da kudade.
“Bincikenmu ya nuna mana cewa sun kai shekaru 3 su na harkar tsakanin Kano, Kaduna, Katsina, Maiduguri da sauran jihohi.”
Muhammad ya ce yanzu haka hukumar su ta umarci jami’ansu da tsayawa tsayin-daka wurin kama sauran ‘yan kungiyar, kamar yadda ya zo a ruwayar ta The Nation.
Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13
Ya kara da sanar da yadda su ka mika su hannun ‘yan sanda don a yanke musu hukuncin da ya yi daidai da abinda su ka aikata.
Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba
A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.
‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.
Asali: Legit.ng