Da Duminsa: An gano gawar ɗan jaridar Nigeria, Salem, da ya ɓace

Da Duminsa: An gano gawar ɗan jaridar Nigeria, Salem, da ya ɓace

  • Rundunar yan sanda sun gano gawar wani dan jaridar, Tordue Salem, da ya bace cikin watan Oktoba
  • Bayan bacewarsa wani lamba boyayye ya kira matarsa yana neman a biya kudin fansa Naira miliyan 100
  • Daga bisani da yan sanda suka tsananta bincike sun gano cewa wani matashi mai shekaru 25 a PortHarcourt ne ya kira wayar

Abuja - An gano gawar dan jaridar Vanguard da ke dakko rahotanni daga Majalisar Tarayya, kimanin wata daya dabacewarsa.

An yi wa Tordue Salem ganin karshe da ransa ne a kusa da gidan man Total da ke kusa da hedkwatar rundunar yan sanda ta Abuja a ranar 13 ga watan Oktoban 2021.

Da Duminsa: An gano gawar ɗan jaridar Nigeria, Salem, da ya ɓace
An gano gawar ɗan jaridar Nigeria, Salem, da ya ɓace. Hoto: Vanguard NGR
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Asirin kuɗi: An kama wani mutum da ya haɗa baki da malamin addini mai shekaru 95 don kashe ɗan cikinsa

Har yanzu dai babu cikakken bayani kan abinda ya yi sanadin mutuwarsa a cewa jaridar Vanguard.

An kama wasu mutane ciki har da wani Prince Enyenihi da ake zargi da hannu a bacewarsa.

An rahoto cewa Enyenihi ya tuntubi matar mammacin yana neman a biya Naira miliyan 100 domin fansar sa.

A cikin sakon kar ta kwana da Enyenihi ya aike wa matar Salem ya ce:

"Idan baki biya ba, Za a kashe Tordue cikin kwanaki bakwai. Domin karin bayani ki kira wannan lambar."

Kwana daya bayan aika sakon, wata lamba da aka boye da kira matar marigayi Salem. Matar ta nemi a bata mijin suyi magana a waya ta tabbatar yana da rai kafin a fara maganan biyan kudin fansa.

Amma wanda ya kira din ya bawa wani mutum daban wayar ya yi basaja a matsayin mijinta.

Da ta lura cewa muryar ba na mijinta bane, ta bukaci ya fada mata sunan yarsu da ranar da aka haife ta, amma aka gaza bata amsa.

Kara karanta wannan

Barawon waya ya mutu cikin Kurkuku yayin rikicin zama shugaban Fursunoni

Yadda aka kama matashin da ya kira matar Salem

A ranar kuma da yamma, wani boyeyyen lamba ya kira ta yana tambayar ko an sako mijinta. Matar, cikin rudani ta tambayi dalilin da yasa mai kiran ya boye lambarsa.

Daga baya yan sanda sun yi bincike sun gano lambar wayar na wata mata ne da ke zaune Port Harcourt, Jihar Rivers.

Amma, matar bayan an kama ta tace ba ruwanta cikin lamarin, tana mai cwa ita ma wannan lambar ya fara kiran ta tun 26 ga watan Oktoba.

Bayan tsananta bincike, mutumin mai suna Enyenihi mai shekaru 25 ya amsa cewa shine ya dauki wayar makwabciyarta ya aika sakon kar ta kwana ba da sanin ta ba bayan ya ga sanarwar neman dan jaridar.

Ya ce ya san ba za a biya kudin fansar ba amma ya yi hakan ne domin ya hukunta makwabciyarsa saboda rashin mutunci da ta ke masa.

Yan sandan sun ce wannan kamen wani yunkuri ne na kawar da hankalinsu daga ainihin masu laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164