Da dumi-dumi: Bayan shafe kusan watanni hudu a hannunsu, yan Boko Haram sun saki ma'aikacin gwamnatin Yobe
- Yan ta'addan Boko Haram sun saki wani jami'in gwamnatin jihar Yobe, Ali Shehu Mai Lalle, da abokinsa da suka yi garkuwa da su
- Mai Lalle da Mustapha sun samu yanci bayan sun shafe kimanin watanni hudu a hannun yan ta'addan
- Sai dai babu wani jawabi daga mahukunta game da sakin nasu a daidai lokacin kawo wannan rahoton
Jihar Yobe - Kungiyar Boko Haram ta saki ma'aikacin gwamnan jihar Yobe, Ali Shehu Mai Lalle, bayan ya shafe kimanin watanni hudu a hannunsu, jaridar The Nation ta rahoto.
Rahoton ya ce wata majiya ta bayyana cewa Mai Lalle ya samu yanci a yanzu inda ya koma ga iyalansa.
Majiyar ta kuma bayyana cewa an saki Mai Lalle ne tare da abokinsa, Mustapha wanda aka sace su tare a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar 24 ga watan Yuli.
Majiyar ta ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Mutuminmu Mai Lalle ya tsira a yanzu yana hannun iyalansa."
Akwai wani rahoto da ba a tabbatar ba cewa an biya makudan kudaden fansa domin sako mutanen biyu amma yan uwa da abokansu sun ki cewa komai a kan haka.
Sai dai babu wani jawabi daga mahukunta game da sakin nasu a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
Boko Haram sun saki hotunan sojoji da jami'an da suka yi garkuwa da su a Yobe
A baya mun kawo cewa ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP sun saki hotunan sojoji biyu da jami’an hulda na Yobe da suka yi garkuwa da su a hanyar babban titin Damaturu/Maiduguri.
Maharan sun kuma saki katin shaidar wadanda suka sace kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
A katinan shaidar da suka baje kolinsu, biyu daga ciki mallakar Mai Lalle ne, daya na Mustapha yayin dayan kuma ya kasance na Lpcl Oyediran Adedotun na rundunar Sojojin Najeriya.
Asali: Legit.ng