Da ina da iko, da na wajabtawa maza auren mata biyu – Jami’ar bincike
- Wata mutuniyar kasar Kenya mai suna Jame Mugo ta bayyana aniyarta na tilastawa maza auren mata biyu idan da ace za ta samu ikon yin hakan
- Matar wacce ta kasance jami'ar bincike ta koka kan yadda magidanta ke lalata da yan mata a wajen gidajen aurensu
- Ta kuma bayyana cewa da zaran mazan sun ci moriyar ganga sai su koma ga wasu yan matan na daban
Kenya - Wata jami'ar bincike ta bayyana cewa da ace tana da iko, toh da za ta wajabtawa maza auren mata biyu domin rage yawan zinace-zinace da lalata.
A cewar matar 'yar kasar Kenyan, Jame Mugo, dabi'ar magidanta na yin lalata da yan mata a wajen gidajen aurensu na karuwa a kullun.
Matar ta koka da yadda maza mazinata ke barin yan matansu ba tare da komai ba sannan su koma ga wasu bayan sun gama cin moriyar ganga.
Ta rubuta a shafinta na Instagram:
"Da ace ina da iko, da na tilastawa maza auren mata biyu. Wasu mazan na amfani da mata, kananan yara domin samun arziki, zamantakewa da nutsuwar zuciya sannan daga baya su watsar da su."
Ta ci gaba da shawartan yan mata da su nemi masoyansu masu aure su hada su da matayensu domin gudun shan wahala.
"Mata, 'yan mata, ku daina soyayya da magidanta cikin sirri, ku nemi su sada ku da matansu.
"Na san matan da ke far ma yan mata masu soyayya da mazan aure kuma mazansu na da yan mata hudu. matasa, tsoffi da masu aure. Ke kadai ba taron jama'a bace. Mu zamo masu kirki."
Sai dai ba a sani ba ko matar mai 'ya'ya biyu ta fuskanci yaudarar da namiji ne a baya. A yan makonnin da suka gabata, ta kwatanta mutane da karnuka, cewa dabbobin sun fi biyayya.
Ta rubuta:
"Mutane na tambayar dalilin da yasa nake son karnuka. Da wuya mutum ya samu irin biyayyar da zai samu a wajen karnuka daga wajen dan adam. Kare zai tsaya a kabarinka yana haushi da kuka a lokacin da abokin zamanka zai shiga soyayya ta gaba. Kana iya jin bacin rai, kuma babu mai lura da hakan. Amma karenka zai lura kuma ya yi kokarin faranta maka rai. Mutanensu na iya watsi da su, amma karnukansu ba za su taba yasar da su ba."
Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki
A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.
Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.
Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.
Asali: Legit.ng