Kaico: Jami'in NSCDC ya bindige wani mutum a ƙugunsa yayin da ya ke fitsari a kusa da ofishinsu

Kaico: Jami'in NSCDC ya bindige wani mutum a ƙugunsa yayin da ya ke fitsari a kusa da ofishinsu

  • Wani jami'in hukumar tsaro da NSCDC ya bindige wani bawan Allah yayin da ya ke fitsari a kusa da ofishinsu
  • Wasu mutane da abin ya faru a gabansu sun yi tir da harbin suna cewa mutumin ba bata gari bane, lebura ne
  • Mai magana da yawun hukumar NSCDC na Cross Rivers, Solomon John, ya ce ana nan ana bincike a kan lamarin

Cross River - Jami'in hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Cross Rivers ya bindige wani mutum da ake ce yana fitsari a wani wuri da ke kallon ofishin hukumar a Cross Rivers.

An bindige mutumin mai shekaru 32 mai suna Nwa-Aba ne da asubahin jiya.

Kawo yanzu ba a gano jami'in da ya bindige mutumin ba kamar yadda ya zo a rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Yadda ginin Ikoyi mai hawa 21 ya rushe, Leburan da ta rutsa da shi ya magantu

Kaico: Jami'in NSCDC ya bindige wani mutum a ƙugunsa yayin da ya ke fitsari a kusa da ofishinsu
Jami'in NSCDC ya bindige wani mutum a ƙugunsa yayin da ya ke fitsari a kusa da ofishinsu. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wanda abin ya faru a idonsu sun magantu

Wani ganau ya ce an harbi Nwa-Aba sau biyu ne a kugunsa a yayin da ya ke fitsari kimanin mita 50 daga ofishin na NSCDC.

Ya ce:

"Yana fitsari a wani wuri ne a lokacin da jami'in NSCDC ya harbe shi a kungunsa. Lebura ne da ke aiki a tashan direbobin tankan man fetur. An garzaya da shi asibiti amma ba mu san halin da ya ke ciki ba yanzu."

Wani Bright Uzo wanda shima ganau ne ya yi Allah wadai da harbin, yana mai cewa akwai yiwuwar wanda ya yi harbin ya kashe Nwa-Aba.

Uzo ya ce:

"Ana zargin ya taho aikata wani laifi ne? Sun harbe shi kafin sanin cewa fitsari kawai ya ke yi. Ko da a kofar ofishinsu ya ke, bai kamata su harbe shi ba. Ba mai laifi bane, kawai fitsari ya ke yi."

Kara karanta wannan

Kwamitin da yake bincike a kan rikicin EndSARS yace dole a kawo Abba Kyari gabansa

Harbin ya janyo zanga-zanga

Jardidar The Nation ta rahoto cewa harbin mutumin da aka yi ya janyo zanga-zanga inda matasa suka nemi a yi wa mutumin adalci a nemo masa hakkinsa.

Wasu jami'an NSCDC dauke da makamai sun tarwatsa masu zanga-zangar.

Mai magana da yawun NSCDC a jihar, Solomon John ya ce ana bincike kan lamarin a halin yanzu.

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164