Tsohon Sarkin Kano Sanusi yace sabon littafinsa da zai fito a 2022 zai gigita ‘Yan siyasa

Tsohon Sarkin Kano Sanusi yace sabon littafinsa da zai fito a 2022 zai gigita ‘Yan siyasa

  • Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yace yana rubuta wani littafi da zai fito a shekarar 2022.
  • Malam Sanusi II ya bayyana cewa yana bi a hankali ne saboda gudun ya taba wasu ‘yan siyasa.
  • Littafin zai yi bayanin yadda aka huro masa wuta a CBN saboda tsarin bankin addinin musulunci.

Africa - Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya kyankyasa cewa yana rubuta wani littafi wanda yake sa ran cewa zai fito cikin nan da shekaru biyu.

Mai martaba Muhammadu Sanusi II yake cewa littafin na sa zai tada hankalin ‘yan siyasa gabanin babban zaben da za ayi a Najeriya a shekarar 2023.

Khalifan na Tijjaniya ya yi wannan bayani ne a wajen wani babban taro da aka shirya a kan harkar tattalin arziki na tsarin addinin musulunci na Afrika.

Kara karanta wannan

Rushewar Ginin Legas: Sun hanani aiki a wajen don ni Musulmi ne, bayan awa biyu ginin ya rushe

Legit.ng ta samu halartar wannan taro, inda tsohon gwamnan na CBN ya tabo wasu batutuwa da dama.

Sanusi II yace a littafin da yake rubutawa, akwai shafi kacokam da ya ware a kan tattalin arziki na tsarin addinin musulunci, da irin kalubalensa da amfaninsa.

Tsohon Sarkin Kano
Tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II Hoto: BBCNewsHausa
Asali: Facebook

CBN: Abin da Sanusi II ya fada a taron

“Ina bi sannu a hankali yanzu ne saboda ba na so in batawa wasu ‘yan siyasa rai a shekarar 2020.” – Sanusi II.
“Idan har ka karanta labaran a littafin, za kayi mamakin irin abin da mutanen nan za su iya yi da soki-burutsu a kan tsarin tattalin na musulunci.”

Khalifan na Tijjaniya yake cewa a lokacin da babban bankin CBN zai bada lasisi a fara bankin musulunci a Najeriya, an yi ta yada cewa za a musuluntar da kasa.

Kara karanta wannan

Wani ɗan sanda ya kashe abokan aikinsa ƴan sanda 4, ya kuma yi wa wasu 3 mummunan rauni

“Har ta kai jami’an DSS sun yi shiri, ana tsoron a samu matsalar rashin tsaro. An nemi shugaban kasa ya sauke gwamnan CBN saboda zaman lafiya.”

Ana amfani da addini a Najeriya

“A Najeriya, addini makamin siyasa ne, ka duba abin da ake yi a yau; ana batun shugaban kasa ya fito daga Arewa zuwa Kudu.” – Muhammadu Sanusi II.

Masanin tattalin arziki yace babu abin da ya damu talaka da yankin da shugaban kasa zai fito, amma wasu manyan ‘yan siyasa suna ribatar wannan matsala.

Sanusi II ya koma makaranta

A jiya ku ka ji cewa Malam Muhammadu Sanusi II zai yi digiri na uku a bangaren ilmin shari’a. Sanusi II ya fara karatunsa na PhD a jami’ar Landan, kasar Birtaniya.

Duk da yana da tarin ilmi, Tsohon Sarkin bai koshi da ilmi ba, ya koma karatu a jami'ar Landan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng