Tarihin shararren marubucin adabin Hausa, Malam Sa'adu Zungur

Tarihin shararren marubucin adabin Hausa, Malam Sa'adu Zungur

Malam Sa'adu Zungur na daya daga cikin shararrun marubutan adabin Hausa ya kuma kasance dan siyasa a lokutan baya.

Sa’adu ya sha gwagwarmaya wajen yaki da yadda turawan mulkin mallaka suka mulki kasar Najeriya a wancan lokaci. Sannan kuma ya kasance mutun mai kaifin tunani, hazaka da hangen nesa.

An haifi Sa'adu Zungur a watan Nuwamban shekarar 1914 a cikin garin Bauchi. Bayan ya yi karatun Islamiya da kuma na littafafan addinin musulunci, malam ya halarci makarantar kwaleji na Yaba dake birnin Legas a shekarar 1934.

Tarihin shararren marubucin adabin Hausa, Malam Sa'adu Zungur
Tarihin shararren marubucin adabin Hausa, Malam Sa'adu Zungur

Ya zama malamin wata makaranta a garin Zariya bayan ya dawo daga jihar Lagas. Bayan haka ya kuma kafa wata kungiya mai suna Zaria Friendly Society tare da Malam Abubakar Imam da wasu abokansu a wancan lokacin. Kungiyar tasu wacce daga baya ta kasance kamar kungiyar siyasa a yankin ta sha suka daga wasu sarakunan lokacin.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin saman Najeriya ta kuma yaye sababbin matukan jirgin yaki a Kano (hotuna)

A shekara ta 1942 ya sake dawowa garin Bauchi inda ya ci gaba da harkan karantarwa. Bayan gamayya da suka yi da su Malam Animu Kano da Muhammad Baba Halla na yin gwagwarmaya da yadda ake mulki a yankin Arewa a wancan zamanin, Malam Sa'adu Zungur ya kasance sakataren jam'iyar NCNC a shekarar 1948.

Malam Sa'adu ya yi rubuce-rubuce da dama a fannin adabin Hausa. Wasu daga cikin litattafan da ya rubuta wanda suka shahara sun hada da:

1. Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya

2. Maraba Da Soja

Ya kuma kasance abun kwaikwayo ga wasu marubutan adabin Hausa irin su Malam Abubakar Ladan Zariya da sauran marubuta.

Allah ya amshi ran Malam Sa'adu Zungur a shekarar 1958 a cikin garin Bauchi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng