'Kwararan Hujjoji 4 Da Mai Yiwuwa Suka Sa Maina Murmushi Bayan Yanke Masa Ɗaurin Shekaru 8 a Kotu
- Ba boyayyen abu bane batun yadda mutane su ka dinga cece-kuce bayan bidiyon Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa na kotu ya bayyana
- A cikin bidiyon, an hango Maina cike da annashuwa da murna yayin da jami’an hukumar gidan gyaran hali suka tasa keyarsa zasu wuce da shi
- A wannan labarin an tattaro kwararan dalilan da ake zargin sun ja tsohon shugaban hukumar fanshon ya nuna rashin damuwar sa hasali ma sai murna
Abuja - Babbar kotun da ke zama a Abuja a ranar Litinin 8, ga watan Nuwamba ta yanke wa Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa shekaru 8 a gidan gyaran hali.
An zargi Maina da wawuran kudade Naira biliyan 2 na kudin fansho, wanda bayan tabbatar da laifukan da ake zargin sa da shi aka yanke masa hukunci.
Jim kadan da yanke hukuncin aka hango Maina ya na murmushi yayin da jami’an hukumar gidan gyaran hali suke tasa keyarsa a wani bidiyo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A tsokacin da wasu ‘yan Najeriya da dama suka dinga yi karkashin bidiyon, sun nuna mamakin su dangane da karfin halin Maina.
Legit.ng ta tattaro wasu dalilai 4 kwarara da ake zargin su ne sabubban murmushin Maina duk da halin da ya tsinci kan sa.
Tushen lamarin
Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta zargi Maina da damfarar gwamnatin tarayya Naira biliyan 2.1 wanda bayan gabatar da korafin, kotu ta yanke hukunci.
Kotu ta bukaci kwace kadarorin Maina da ke Abuja, manyan motocinsa da sauran su. Har ila yau gwamnati za ta amshe kamfanin sa mai juya N1.8bn kuma kimar sa ta kai $537,983, duk a cikin kwana 90.
Ga dai dalilan da dan jaridar Legit.ng ke ganin ta yi wu suka saka Maina murmushi:
1. Duk da kudaden da kotu ta amshe ta yiwu akwai wasu kudade da ya adana a wasu wuraren daban
Zai yuwu murmushin sa na nuna yadda ya tura wa wani daban don ya kalmashe ma sa wasu kudaden ma su yawa, hakan kadai ya isa sa shi farinciki.
2. Saura mishi shekaru 5 a gidan yari tunda a tirka-tirkar an kwashe shekaru 3 yanzu haka ana yi
Ka san an hukunta ka akan satar Naira biliyan 2 kuma hukuncin ka shekaru 8 ne, kuma a haka ka kwashe shekaru 3, shin ba za ka ji dadi ba?
Hakan kadai ya isa ya kwantar ma sa da hankali kuma ya sa shi farinciki har zuciyarsa yayin da fuska za ta bayyana.
3. Ta yuwu kuma murmushin bai kai zuciya ba
Maimakon ya nuna takaicin sa duk da hukuncin ya yi masa zafi, ta yuwu murmushin yake ya ke yi. Kuma ya yi amfani da murmushin wurin kwantar wa da kan sa hankali.
4. Ta yiwu ya gano wata hanya wacce zai yi rayuwa a gidan yari cikin kwanciyar hankali
Duk da wannan ba lallai ya tabbata ba, amma babu abinda ba zai iya yuwuwa ba. Ta yiwu Maina ya nemo wasu hanyoyin da zai more rayuwa a gidan gyaran halin ne.
Motocci Fiye Da 50, Gidaje a Dubai Da Amurka: Jerin Kadarori Da Kuɗi Da Maina Ya Mallaka a Cewar EFCC
A wani rahoton, kun ji cewa A ranar Litinin, 8 ga watan Nuwamba, Hukumar Yaki da Masu Yi wa tattalin arziki ta'annati, EFCC, ta yi nasara kan karar da ta shigar kan Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar yi wa tsarin fansho garambawul, PRTT, kan wawushe kudin fansho fiye da N2.1bn.
An samu Maina da laifuka kan zargi na 2, 3, 6, 7, 9 da 10 da EFCC suka tuhume shi da aikatawa, kana kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 8 a gidan gyaran hali.
Mai shari'a Okon Abang na Kotun Tarayya da ke Birnin Tarayya Abuja ya bada umurnin a kwace wasu kudade da kadarori mallakar Maina.
Asali: Legit.ng