Da duminsa: Yan bindiga sun kaiwa tsohon Soja AVM Maisaka hari gidansa dake Rigasa, sun hallakashi da jikansa

Da duminsa: Yan bindiga sun kaiwa tsohon Soja AVM Maisaka hari gidansa dake Rigasa, sun hallakashi da jikansa

  • Babban jami'in Sojin mai ritaya ya rasa rayuwarsa sakamakon harin da wasu tsagerun yan bindiga suka kai gidansa
  • Uwargidar mamacin ta bayyana cewa kashe Sojan kawai sukayi basu sace kowa ko komai ba
  • Marigayin ne mammalakin MSK dake Makarfi Road, Rigasa a Kaduna

Igabi LGA, Kaduna - Wasu tsagerun yan bindiga sun hallaka wani tsohon Sojan sama, Air Vice Marshal, Mohammed Maisaka, a gidansa dake unguwar Rigasa a jihar Kaduna.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa yan bindiga sun bindigeshi tare da jikansa, Mohammed Musa, wanda shima Soja ne.

Wani mazaunin unguwar da Legit Hausa ta tuntuba ya bayyana cewa dogarinsa ne aka kashe ba jikansa ba.

An tattaro cewa yan bindigan sun dira gidan da daren Litnin misalin karfe 8:30 na dare kuma suka harbesu har lahira.

Kara karanta wannan

Buhari ya nemi majalisa ta amince da Farfesa Omotayo a matsayin DG na NIPSS

Uwargidar marigayin, Hajiya Fatima Maisaka, ta bayyana cewa basu dauki komai daga gidan ba, a cewar DailyTrust.

"Sun shigo ne kawai cikin daki suka kashesu ba tare da daukan komai ba. Ko wayoyinmu basu kwace ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da duminsa: Yan bindiga sun kaiwa tsohon Soja AVM Maisaka hari gidansa dake Rigasa, sun hallakashi da jikansa
Da duminsa: Yan bindiga sun kaiwa tsohon Soja AVM Maisaka hari gidansa dake Rigasa, sun hallakashi da jikansa
Asali: Original

Malam Bashir, wanda makwabcin marigayin ne ya bayyana mana yadda abin ya faru.

Yace:

"A gida suka harbeshi da dogarinshi, mutum biyu kawai aka kashe. Shine mai asibitin MSK."
"Kafin yayi ritaya shine shugaban asibitin Airforce. Ba masu garkuwa da mutane bane, kawai kasheshi suka zo yi."

Tuni ba shi da lafiya, bai dade da dawowa ba

Bashir ya kara da cewa can dama bai da lafiya kuma bai dade da dawowa ba daga kasar Indiya inda yaje jinya.

"Bai da lafiya ma, bai dade da dawowa ba daga Indiya, saboda haka bamu san abinda yayi musu ba amma bincike zai bayyana gaskiya," ya kara

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da ma'aikatan gwamnatin Kaduna a Zaria, dukkansu mata

Yan bindiga sun yi awon gaba da ma'aikatan gwamnatin Kaduna a Zaria, dukkansu mata

A wani labarin kuwa, tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da iyaye mata ma'aikatan gwamnatin jihar Kaduna yayinda suke hanyar tafiya cikin mota.

Daily Nigerian ta bayyana cewa wannan abu ya auku ne da yammacin Litinin misalin karfe 5 tsakanin Giwa da Zaria.

Rahoton ya kara cewa direba kadai yan bindiga suka saki ya tafi domin ya sanar da gwamnatin jihar da iyalansu abinda ya faru.

Legit ta tabbatar da wannan abu daga bakin wasu iyalan ma'aikatan da aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: