Shekarun sun yi kadan: Martanin yan Najeriya a kan hukuncin da kotu ta yanke wa Maina
- Jama'a sun yi cece-kuce a kan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina
- Sun ce hukuncin daurin shekaru takwas kacal ya yi kadan ga mutumin da ya aikata laifin satar kudaden talakawa
- Justis Okong Abang ne dai ya yanke wa Maina hukuncin daurin shekaru takwas bayan an same shi da laifin satar sama da biliyan 2 na yan fansho
Bayan hukuncin daurin shekaru takwas da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon shugaban hukumar Fansho, Abdulrasheed Maina, sakamakon kama shi da laifin sata, ‘yan Najeriya da dama sun tofa albarkacin bakunansu.
Alkalin kotun, Okong Abang ne ya zartar da hukuncin, inda ya ce kotun ta kama Maina da laifin satar kudi sama da biliyan 2 na 'yan fansho "wadanda da yawansu sun rasu kuma basu ci guminsu ba", rahoton Premium Times.
Sai dai wannan hukunci bai birge yan Najeriya da dama ba domin suna ganin wannan hukunci da aka yanke wa Maina ya yi kadan.
A bisa ga ra’ayin wasu, sun ce kamata yayi a dunga yanke wa wadanda aka kama da laifin satar kudaden jama’a hukuncin daurin rai da rai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Martanin ‘yan Najeriya
Legit Hausa ta zakulo martanin wasu daga cikin mabiya shafinta na Facebook a kan wannan al’amari.
Mohammed Ibrahim ya yi martani:
"Mutum akamashi da satar kudi har N2 Billion amma hukuncin shekara takwas Kawai!!
"To amma abun tamabayan anan shine zai dawo da Kudin?"
Khaleepha Khalee ya ce:
"abun dariya arne ya daure musulmi kaga yana nuna masa cewa yafishi tsoran Allah"
Saddiquh Isah ya ce:
"duk wanda aka kama da satan kudin talakawa akaisa life in prison Amman idanba haka aka faraba wallahi inazuwa saina debama yan uwana nasu."
Auwerl Abdulmumin ya ce:
"Insha Allahu bazaigama da duniya lpy ba... Kuma wlh hakkin mutane bazai bari ya kwanta a kabari lpy ba"
Benedict Murphy ya ce:
"Shekara takwas kadai? Wanda ya data #1000 ko mudun Masara daya, hour nawa zai yi a gidan gyaran hali?"
Kotu ta janye belin Faisal Maina, ta bukaci a damko shi
A wani labari na daban, a ranar Talata, babbar kotun tarayya ta Abuja, ta umarci a kama yaron tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, Faisal, bayan kin bayyanarsa a kotu don a cigaba da shari'a a kan zargin ha'inci da ake masa.
Alkali mai shari'a, Okon Abang, ya umarci jami'an tsaro da su kama Faisal duk inda suka gan shi.
Kotun ta gayyaci wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaura-Namoda, Umar Galadima, don ya bayyana a gabanta ranar Laraba.
Asali: Legit.ng