Ana kashe mutane, Shugaba Buhari zai yi bayani gaban Allah inji Tsohon Gwamna, Bafarawa
- Tsohon gwamnan jihar Sokoto yace mutanen Arewa maso yamma suna cikin bala’in rashin tsaro.
- Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana cewa jama’a ba su da damar kawo kayan gonansu gida a yau
- ‘Dan siyasar yace ana fama da yunwa, sannan an rufe hanyoyin sadarwa da kasuwanni a garuruwa.
Sokoto - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage a kan matsalar rashin tsaro.
Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa yace a halin yanzu yankin Arewa maso yamma yana cikin masifa. Bafarawa ya bayyana haka da BBC tayi hira da shi.
Babban ‘dan siyasar ya koka kan halin da mutanen yankin na sa da na shugaban kasa ke ciki. Jaridar Vanguard ta bibiyi hirar da aka yi da Bafarawa jiya.
Abin da Attahiru Dalhatu Bafarawa ya fada
“Sha’anin rashin tsaro wani bala’i ne da ya auko mana. Mutanen da ke can ne kurum za su iya bayanin halin da ake ciki a Sokoto da Zamfara.” – Bafarawa.
“Abin takaicin shi ne tsaron kasa na kan wuyan gwamnatin tarayya ne. Masu fadawa Buhari abubuwa suna tafiya daidai (ko suna ce masa da matsala ne?).”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Idan suna fada masa abubuwa suna tafiya daidai ne, sun cuce sa, kuma sun cuce mu.”
Attahiru Dalhatu Bafarawa yake cewa Allah (SWT) ya san cewa ana cikin mummunan yanayi a yankinsa na Arewa maso yamma, domin mutane suna kuka.
Babu wanda ya isa ya shiga gonarsa - Bafarawa
“Yau, na je gida na dawo, na shaida da idanuna (ba fada mani aka yi ba). Mutane sun noma shinkafa da gero, amma ba za su iya kai amfaninsu gida ba.”
Tsumagiyar Kan Hanya: Barayin da suka sace masu ibada 60 a Kaduna sun bukaci buhunan shinkafa da jarkokin mai
“Duk wanda ya je gona ya dauko kayan noman da ya samu, ba zai dawo da rai ba. A irinsu Zamfara, an tsare mutane, babu waya, kuma an rufe kasuwa.”
Da aka tambayi Bafarawa ko adawa ce ta sa shi yake irin wadannan maganganu, sai yace lamarin ya shafi har shugaban kasa, kuma Allah (SWT) zai tambaye shi.
Ana garkuwa da mutane a Arewa
Ko a farkon makon nan, kun ji cewa miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da wasu masallata a baya-bayan nan a karamar hukumar Mashegu da ke jihar Neja.
'Yan bindigan sun sake yin garkuwa da mutane biyu da suka tafi kai musu lemu da kayan abinci.
Asali: Legit.ng